Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ware filaye ga matasa 1,000 daga ƙananan hukumomi 44 na jihar, a wani muhimmin shiri da aka tsara domin ƙarfafa matasa, bunƙasa mallakar gidaje, samar da dukiya da kuma ba su damar samun makoma mai inganci.
Da yake wakiltar Gwamna Abba Kabir Yusuf wajen rabon takardun filayen a Coronation Hall da ke Gidan Gwamnati a Kano, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Farouk Umar Ibrahim, ya ce shirin ya nuna ƙudurin gwamnatin na samar wa matasa kadarori da damar dogaro da kansu ta fuskar tattalin arziki.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa makomar Kano tana da alaƙa sosai da ci gaban matasanta, yana mai cewa gwamnati mai hangen nesa dole ta zuba jari wajen samar wa matasa damarmaki na mallakar kadarori, gina dukiya da kuma taka rawa wajen ci gaban al’umma.
Ya ce fili na daga cikin muhimman kadarorin da mutum zai iya mallaka saboda darajarsa na ƙaruwa, yana samar da damar tattalin arziki, sannan ya zama ginshiƙin tsaron makomar iyalai da gina dukiya mai ɗorewa.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa ba kawai filaye aka bai wa matasan ba, illa filaye ne da ke cikin tsare-tsaren gine-gine da gwamnati ta amince da su, waɗanda aka tsara da tanadin hanyoyi, magudanan ruwa, makarantu, cibiyoyin lafiya, wuraren ibada, kasuwanni, wuraren shakatawa da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.
Ya kuma buƙaci waɗanda suka amfana da su ɗauki takardun rabon filayen a matsayin wata dama ta mutunci da tsaro, su kare filayensu, su guji sayar da su don neman riba cikin gaggawa, sannan su gina su gwargwadon ƙarfinsu.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Filaye da Tsare-tsaren Gine-gine, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ya ce shirin na da nufin samar wa matasa kadarorin da za su kasance ginshiƙin mallakar gidaje, kafa sana’o’i da samar da dukiya mai ɗorewa.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta tsaurara yaƙi da masu ƙwace filaye ba bisa ƙa’ida ba, wato “Awan Igiya”, tare da ƙoƙarin kwato filayen gwamnati da gurfanar da masu laifi a gaban kuliya.
Ya buƙaci matasan da su kiyaye takardunsu, su bi ƙa’idojin gini da aka amince da su, tare da guje wa sayarwa ko mika filayen ba bisa ƙa’ida ba.
Masu cin gajiyar shirin sun gode wa Gwamna Yusuf, inda suka ce rabon filayen zai taimaka musu wajen gina gidaje, kafa sana’o’i da tabbatar da makomar iyalansu
