Nijeriya na buƙatar haɗin kai yanzu fiye da kowane lokaci – Idris

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ɗaukaka tunaninsu sama da bambance-bambancen addini, ƙabila da siyasa, tare da haɗa kai wajen yaƙi da rashin tsaro da sauran ƙalubalen da ke fuskantar ƙasar.

Idris ya yi wannan kiran ne ranar Talata a Abuja, yayin wani taron ƙasa da ƙasa mai taken “Bambance-bambance da Zaman Lafiyar Al’umma: Haɗin Gwiwa don Kyakkyawar Makoma”, wanda ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iƙamatus Sunnah (JIBWIS) ta shirya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar ƙasashen Musulmi ta Duniya.

Ministan ya ce bambance-bambancen da ke tsakanin ’yan Nijeriya bai kamata ya zama sanadin rarrabuwar kai ba, yana mai cewa tsaro, zaman lafiya da wadata a ƙasar sun dogara ne da yadda ’yan ƙasa za su yi aiki tare.

“Dukkanmu muna buƙatar mu haɗa kai, mu yi tunani a matsayin ’yan Nijeriya, mu yi tunani a matsayin ’yan Adam, kuma mu yi aiki tare ba tare da la’akari da bambance-bambancenmu ba, domin mu kasance tsintsiya maɗaurin ki ɗaya,” inji shi.

Ya jaddada cewa shigar da bambance-bambancen addini da ƙabila cikin yaƙin da ake yi da rashin tsaro na iya ƙara dagula matsalar, yana mai kira ga ’yan Nijeriya da su yi watsi da tashin hankali da rashin haƙuri.

“Babu lokacin bambance-bambance. Idan a yayin yaƙin da muke yi da rashin tsaro muka bari bambance-bambancen addini suka shiga, hakan zai ƙara dagula matsalar. Buƙatar da muke da ita ta haɗa kanmu a matsayin al’umma ɗaya na da matuƙar muhimmanci,” inji Ministan.

Idris ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ita ce ta shirya taron ba, sai dai gwamnati tana maraba da duk wani shiri da ke inganta tattaunawa tsakanin mabiya addinai, zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Ya ce idan ’yan Nijeriya na son samun ci gaba da wadata, dole ne su haɗa kai wajen fuskantar matsalolin ƙasar.

“Idan muna son ci gaba da tafiya zuwa ga wadata, dole ne dukkanmu mu yi tunani da aiki tare, mu kuma haɗa kai a matsayin al’umma ɗaya,” inji shi.

Ministan ya kuma bayyana cewa muhimmancin Nijeriya da yawan al’ummarta ya sa zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƙasar ke da tasiri ga Afirka da sauran sassan duniya.

“Nijeriya ƙasa ce mai matuƙar muhimmanci. ƙasa ce mai mutane sama da miliyan 230. Zaman lafiya da kwanciyar hankali a nan na nufin zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk faɗin Afirka, har ma da duniya baki ɗaya,” inji shi.

Tinubu ya jaddada buƙatar haɗin kan ƙasa

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, wanda ya wakilci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a wajen taron, ya isar da saƙon aniyar shugaban ƙasar na tabbatar da ingantaccen tsaro mai ɗorewa, haɗin kan ƙasa da ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

Ya ce Nijeriya za ta ci gaba da aiki tare da abokan hulɗarta na ƙasa da ƙasa wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Shi ma Babban Sakataren ƙungiyar ƙasashen Musulmi ta Duniya kuma Shugaban ƙungiyar Malaman Musulunci ta Duniya, Sheikh Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa, ya buƙaci ’yan Nijeriya da su kare haƙƙin ɗan Adam da suka yi tarayya a cikinsa.

Al-Issa ya kuma yi kira da a yi watsi da duk wani yunƙuri na amfani da addini, ƙabila ko talauci wajen raba kan ƙasa.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya yi kira da a ci gaba da tattaunawa da tsare gaskiya wajen magance ƙalubalen da ke fuskantar Nijeriya.

Ya buƙaci ’yan Nijeriya da su sake gina amana tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin mabiya addinai domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

A nasa jawabin, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya buƙaci ’yan Nijeriya da su ɗauki bambance-bambancen da ke akwai a ƙasar a matsayin tushen ƙarfi, ba abin da zai raba su ba.

Ya ce duk da cewa ’yan Nijeriya suna gudanar da ibada ta hanyoyi daban-daban, suna da buri da ƙalubale iri ɗaya da ya kamata su haɗa kai wajen fuskanta.

Shugaban JIBWIS na ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi kira da a ƙara haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, ƙungiyoyin addini da al’ummomi wajen yaƙi da rashin tsaro.

Sheikh Lau ya kuma jaddada muhimmancin ƙara zuba jari a fannin ilimi da bunƙasa ƙwarewar matasa domin rage yiwuwar matasa su rungumi tsattsauran ra’ayi ko shiga ayyukan laifi.

Taron ya samu halartar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin; Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani; Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi; Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum; Ministan Bunƙasa Kiwo, Idi Mukhtar Maiha; Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III; Shugaban APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda; Sheikh Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa; Sheikh Abdullahi Bala Lau da sauran manyan jami’an gwamnati, shugabannin addinai da na gargajiya, jami’an diflomasiyya da wakilan ƙungiyoyin fararen hula.

By ukarofi

Leave a Reply