‘Yan bindiga sun halaka matafiya tara a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan sanda sun gano wasu gawarwaki na mutane guda tara waɗanda ake zargin ‘yan bindiga ne suka halaka su a akan hanyar Wawa zuwa Lumma da ke Ƙaramar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.

Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito cewa jami’an ‘yan sanda da sojoji da aka tura yankin sakamakon aun labarin ne suka gano a ranar Talata.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa NAN a Minna cewa
jami’an tsaron sun kwashe gawarwakin daga wurin, yayin da aka ƙara tsaurara ayyukan sintiri da bincika wuraren da ake zargin ‘yan bindiga na amfani da su wajen fakewa.

Abiodun ya kuma ce, an ƙara yawan adadin jami’an tsaro a hanyar Wawa-Lumma da yankunan da ke kewaye da ita domin hana sake faruwar irin wannan harin da kuma tabbatar da tsaron matafiya.

Wannan lamari na zuwa ne yayin da ake ƙara nuna damuwa kan matsalar tsaro a yankin, musamman bisa la’akari da yadda matafiya ke fuskantar barazanar hare-haren ‘yan ta’adda.

Kazalika, hanyar na ɗaya daga cikin hanyoyin da ke haɗa wasu yankunan jihar Neja, kuma aukuwar irin waɗannan hare-hare a wasu sassan jihar sun jefa matafiya da mazauna yankunan cikin fargaba.

A ƙarshe, rundunar ‘yan sandan ta ce ayyukan jami’an tsaro za su cigaba da gudana a yankin domin gano masu hannu a kisan da gurfanar da su ga doka tare da tabbatar da samun cikakken tsaro a yankin da ma jihar baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply