Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
An shawarci gwamnatin Kano da sauran gwamnatoci har zuwa matakin tarayya da su riƙa tuntuɓar manoma na haƙiƙa kafin su raba tallafin noma, musamman takin zamani da sauran kayan aikin gona kamar taraktoci da makamantansu.
An bayyana cewa akwai buƙatar gwamnatoci su riƙa tuntuɓar ƙungiyoyin manoma na gaskiya waɗanda aka tabbatar da cewa manoma ne, domin samun nasarar duk wani shiri na tallafin noma da kuma cimma manufofin gwamnati na bunƙasa tattalin arziki, samar da abinci da ci gaban jihohi da Nijeriya baki ɗaya.
Wannan shawara ta fito ne daga bakin shugaban ƙungiyar Masu Sayar da Taraktocin Noma da Makamantansu ta Arewa, Ambasada Mai Kudi Ahmad Kadawa, a lokacin da yake ganawa da manema labarai a birnin Kano a ƙarshen makon da ya gabata.
Haka kuma, ya yaba wa gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa bayar da tallafin takin zamani a farashi mai sauƙi, inda aka rage farashin da kusan kashi 45 cikin 100.
Ya ce wannan mataki abin yabawa ne, amma a matsayinsu na manoma, suna ganin ya dace gwamnati ta tuntubi ƙungiyoyin manoma tare da sanya sarakuna cikin tsarin rabon tallafin, kamar hakimai, dagatai, masu unguwanni, limamai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar shugabanci da noma.
A cewarsa, idan aka bi wannan tsari, nasarar da za a samu za ta ninka sau 100, duk da cewa gwamnati ta sanya hukumomin da take ganin za su hana karkatar da tallafin zuwa wani wuri.
Ya ce duk da matakan da gwamnati ta ɗauka, har yanzu ana samun zarge-zarge da koke-koke daga wasu wurare bayan rabon takin gwamnatin Kano, lamarin da ya ce ya kamata a duba domin tabbatar da cewa tallafin ya isa ga waɗanda aka yi niyyar taimakawa.
Ambasada Mai Kudi ya ce akwai buƙatar gwamnatin Kano da sauran gwamnatocin jihohi su riƙa bin wannan tsari domin tabbatar da manufofinsu na bunƙasa noma da samar da isasshen abinci a Nijeriya.
Haka zalika, ya ƙara da cewa manoma su ne suka fi sanin nau’o’in takin da ake buƙata a lokuta daban-daban, ciki har da takin NPK da takin urea, da kuma irin amfanin da kowannensu ke yi.
Ya ce bai kamata a dogara kawai da waɗanda suka yi karatu a fannin noma ko wasu jami’an gwamnati ba, domin manoma masu aiki a gonaki su ne suka fi sanin matsalolin da suke fuskanta a aikace.
Dangane da gwamnatin tarayya, Ambasada Ahmad Kadawa ya yi kira ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ƙara ƙoƙari wajen inganta harkokin tsaro, yana mai cewa rashin tsaro ya yi matuƙar illa ga harkar noma a yankin Arewa.
Ya ce sakamakon rashin tsaro, kusan kashi 30 cikin 100 na manoman Arewa ne kawai ke iya gudanar da noma yadda ya kamata.
Ya bayar da misalin wani manomi da ya noma gonarsa da ke da nisan kilomita biyar daga inda yake zaune, amma daga baya ya gudu ya bar gonar sakamakon harbe-harbe da barazanar ’yan bindiga.
A cewarsa, hakan na nufin an yi asarar aikin da manomin ya gudanar tare da kuɗin da ya kashe.
Ya ce ban da rashin tsaro, akwai kuma wasu matsaloli da ke ƙara jefa harkar noma cikin mawuyacin hali, ciki har da ƙarancin darajar amfanin gona, tsadar taki da iri, da sauran kayan aikin noma.
Ya jaddada cewa noma shi ne ginshiƙin ci gaban kowace ƙasa, musamman wajen samar da abinci ga ’yan ƙasa.
Ambasada Kadawa ya kuma koka kan yadda rashin tsaro ya shafi sana’ar masu sayar da motocin noma da sauran kayan aikin gona, inda ya ce a wasu jihohi ’yan kasuwa kan samu masu son sayen kayan aikin, amma rashin tsaro ya sa tafiya zuwa wuraren ba ta yiwuwa.
Sai dai ya bayyana cewa abin ƙarfafa gwiwa shi ne yadda fasahar noma ke ci gaba da bunƙasa a duniya, inda Nijeriya ma ke samun ci gaba wajen amfani da sabbin fasahohin noma idan aka kwatanta da shekarun baya.
A ƙarshe, shugaban ƙungiyar Masu Sayar da Motocin Noma da Makamantansu ta Arewa, Ambasada Mai Kudi Ahmad Kadawa, wanda tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano ne mai wakiltar ƙaramar Hukumar Ungogo, ya yabawa gwamnatin tarayya bisa rahotannin cewa ta ware ɗaruruwan biliyoyin naira domin tallafawa harkar noma a wannan lokaci.
Ya ce ko da yake ba su samu cikakken bayani kan yadda aka raba kuɗaɗen ba, ko kuma ko har yanzu ba a fara rabawa ba, sun ji rahotannin cewa gwamnati ta ware kuɗaɗen domin tallafawa manoma.
Ya yi kira da a sanya masu ruwa da tsaki a cikin harkar noma cikin duk wani tsari da za a samar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da nasarar shirin da kuma amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata.
