Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
A wani babban sauyi a siyasar Nijeriya, wasu manyan shugabanni daga jam’iyyun New Nigeria Peoples Party (NNPP) da Action Democratic Party (ADP) na jihar Kano, sun sanar da komawarsu zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Sauyin jam’iyyar ya faru ne a wani taro da aka gudanar a gidan Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a birnin Abuja. Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, shi ma yana cikin wadanda suka halarci taron.
Daga cikin fitattun waɗanda suka sauya sheka akwai Sanata Kawu Sumaila; Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ɗan
majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Rano, Kibiya da Bunkure; Hon. Abdullahi Sani Rogo, ɗan
majalisar wakilai mai wakiltar Karaye da Rogo; da kuma Hon. Zubairu Hamza Massu, ɗan majalisar dokoki ta Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Sumaila.
Kazalika, akwai tsofaffin kwamishinoni na Jihar Kano irinsu Hon. Diggol, Hon. Abbas Sani, da Hon. Baffa Bichi, wanda ya riƙe muƙamin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, suma sun shiga jam’iyyar APC. Sannan kuma Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada, tsohon ɗan takarar gwamna a Kano ƙarƙashin jam’iyyar ADP, ya shiga jam’iyyar APC.
