
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani hatsarin kwale-kwale ya yu ajalin kimanin mutane 14 a Ƙaramar Hukumar Yauri da ke Jihar Kebbi.
Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya faru ne a ƙauyen Gumbi da ke Gundumar Gumbi yayi da waɗanda abin ya rutsa da su ke rakiyar amarya zuwa gidan mijinta a ƙauyen Gwarzo da ke Ƙaramar Hukumar Ngaski.
An ruwaito cewa, iftila’in ya auku ne a lokacin da mahalarta bikin suke hanyar koma wa gidajensu, wanda ya jefa sama da fasinjoji 100 cikin kogin.
A yayin haka ne mutane 14 da suka haɗa da mata 13 da ƙaramin yaro ɗaya suka rasu.
Gwamna Nasiru Idris, wanda ya halarci jana’izarsu, ya kuma jajenta wa iyalansu, ƙaramar hukumar, masarautar, da kuma al’ummar Yauri.
Ya kuma yi kira a gare su da su rungumi ƙaddara.
Gwama Idris, wanda ya samu wakilcin Shugaban ƙaramar hukumar, Abubakar Shu’aibu, ya kuma addu’ar Allah ya gafarta musu kurakuransu, ya kuma sanya su a Aljanna Firdausi.
