A guji ɗaukar doka a hannu

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Tun bayan kisan gillar da wasu matasa su uku suka yi wa wata mata mai suna Fatima Abubakar kisan gilla tare da yaranta su shida a unguwar ɗorayi Chiranchi cikin Jihar Kano, a ranar 17 ga watan Janairu, 2026 jama’a da dama suka fusata, duba da ganin yadda aka yi wa iyalin mummunan kisan gilla na rashin imani. Don haka ne ma yayin da aka ce an sake samun wani matashi da ya burma wa wata mata almakashi a ciki, a ƙoƙarin sa na sace mata waya, a cikin wannan unguwar dai ta ɗorayi, wasu fusata fusatattun matasa a unguwar suka far masa tare da kashe shi nan take. Kodayake daga bisani an samu ceto ran wannan baiwar Allah da saurayin ya yi ƙoƙarin kasheta.

Wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaron ’yan sanda ke bibiyar batun kisan gillar da aka yi wa Fatima da iyalinta, a gaban kotu, yayin da jama’a ke ganin jinkirin zartar da hukunci kan makisan da ake zargi, da tafiyar hawainiyar da suke ganin shari’ar na yi a cewarsu. Hakan na iya zama dalilin da ya sa jama’a suka harzuƙa suka fara ɗaukar doka a hannu kan waɗanda ake zargi da aikata ba daidai ba. Sai dai a yayin da wasu ke tunanin hakan shi ne daidai, saboda kada a riƙa barin masu laifi suna samun ’yanci a gaban shari’a, da sunan sun aikata laifin ne cikin rashin lafiyar ƙwaƙwalwa da sauran uzurori da lauyoyi kan gabatar a gaban shari’a. Aiki da hankali yana tabbatar da cewa, ɗaukar doka a hannu babban laifi ne shi ma, domin kuwa alƙali ne kaɗai yake da ’yancin ayyana mutum a matsayin cikakken mai laifi, sakamakon hujjojin da aka gabatar masa da suka tabbatar da abin da ake zargi ƙarara.

Saurin fushi da zartar da hukunci yana sa nadama, domin kuwa garin irin haka ne ake kuskuren yin hukunci ga wanda ba shi ya aikata laifin da ake zargi ba. Kuma ko da ma an tabbatar ɗin, kuskure ne a kama mai laifi nan take a rufar masa da duka har a yi masa ɗanyen hukuncin da bai kamata ba.

Wani rahoto daga ƙaramar Hukumar Bakura a Jihar Zamfara ya bayyana yadda wasu fusatattun matasa suka kashe wani saurayi bayan shi ma ya sari wata mata da adda har ta rasa ranta. Wannan mummunan al’amari ya haifar da firgici da damuwa a zukatan jama’a sosai, musamman duba da halin da jihar ke ciki na taɓarɓarewar tsaro.

Ba da jimawa ba, ƙungiyar kare haƙƙoƙin bil’adama ta Amnesty International Nigeria ta fitar da wani rahoto da ke cewa aƙalla mutane 155 ne aka yi wa kisan gilla ta hanyar ɗaukar doka a hannu a ƙasar nan, cikin shekaru 10 da suka gabata, ba tare da an bai wa doka ko jami’an tsaro damar aikinsu ba. 

Daraktan Amnesty International a Nijeriya, Isa Sanusi, ne ya bayyana cewa, an kashe mutanen ne sakamakon zargin su da ake yi kan ɓatanci ga addini, sata, ko kuma maita, inda yawanci ake kai wa waɗanda ake zargi hari tare da kashe su ba tare da bincike ko bin ƙa’ida ta shari’a ba. Yayin da a cewarsa an kashe mutane 23 a ‘yan shekarun nan sakamakon kisan jama’a a sassa daban-daban na ƙasar.

ƙungiyar ta bayyana waɗannan alƙaluman bincike ne, domin bayyana damuwarta game yadda ake samun ƙaruwar kashe-kashen jama’a da gangan, ba ta dalilin harin ta’addanci ko rikicin ƙabilanci da na addini ko hatsari ba, sai don wani zargi marar tushe, wanda shari’a ba ta tabbatar ba. Dalili kenan da ita ma ƙungiyar ta ƙaddamar da gangamin yaƙi da kisan gilla ta hanyar ɗaukar doka a hannu, wanda a Turanci suka yi wa laƙabi da End Mob ɓiolence Campaign.

Bincike ya nuna cewa, jama’a na ɗaukar doka a hannunsu ne saboda rashin gamsuwa da yadda ’yan sanda da sauran jami’an tsaro ke ɗaukar mataki kan waɗanda ake zargi da aikata laifi. Ko kuma yadda kotuna a Nijeriya suke jan ƙafa da wajen gaggauta yanke hukunci kan waɗanda suke aikata laifukan da suke cutar da jama’a a matsayin al’umma ko kuma a ɗaiɗaiku.

Ko a makon da ya gabata sai dai wasu matasa suka nemi halaka wani saurayi da ake zargi da kashe wata dattijuwa, kishiyar kakarsa a wata unguwa cikin garin Jos. Akwai shekarun da irin wannan ɗaukar doka a hannun ta jawo asarar rayuka da dama a Jihar Legas, sakamakon yawaitar ɓarayi a cikin garin Ikko, wanda har ta kai ga da zarar an ce ga ɓarawo nan sai kawai ka ga zarata sun make wanda ake zargi, sun sa masa taya a ka sun banka masa wuta. Ko da kuwa zargin na wasa ne, an yi ne don tsokana. An samu irin haka ma a jihohin Katsina da Zamfara, inda da zarar an kama wani da zargin kasancewa ɗan bindiga ko mai kai rahoton sirri ga ’yan bindiga, nan take sai ka ga an ƙaddamar masa da kisa ba tare da jiran a miƙa shi ga hukuma ba.

Haka ma a Jihar Kano, akwai rahotannin da suka nuna yadda wasu fusatattun mutane suka nemi kashe wasu matasa da ake zargi da satar waya a cikin a daidaita sahu, wanda sai da ta kai ga wasu masu aiki da hankali sun ƙwace su da ƙyar.

Idan za a iya tunawa a shekarar da ta gabata ne aka yi kisan gillar nan da ya ɗaga hankalin ’yan Arewa, wanda aka kashe wasu mafarauta ‘yan asalin Jihar Kano da suka fito daga Fatakwal, a daidai wani gari da ake kira da Uromi a Jihar Edo. An kashe mutane da dama, sakamakon zargin da ake musu kan cewa, masu garkuwa da mutane ne. A Jihar Kuros Riba, wasu ƙauyawa sun kashe wata mata da ake zargi da maita a shekarar 2023, biyo bayan wani hatsari da ya auku, inda aka riƙa jifanta da duwatsu har aka ƙonata da ranta.

Haka ma, a Jihar Ondo an yi irin wannan kisan gilla kan wani direba wanda gangancinsa ya haifar da asarar rayuka da dama, shi ma an yi masa zargin maita da kasancewa ɗan ƙungiyar asiri, kuma a dalilin haka aka yi masa mummunan rotse aka banka masa wuta.

Manazarta na ganin rashin ɗaukar mataki kan masu aikata irin wannan ɗanyen hukunci shi ma yana ƙara ƙwarin gwiwa ga masu yawan masu aikata kisan gillar suna ganin babu abin da zai faru. Bisa hujjar abu ne da ya faru cikin rubibi, babu wani da za a iya kamawa, sai dai a yi kan mai uwa da wabi.

Lallai jama’a mu kaucewa irin wannan mummunan aika-aika, kuma mu hana faruwarsa a duk inda muka ga alamun zai iya faruwa. Sannan jama’a su riƙa haɗa kai da jami’an tsaro suna gaggawar sanar da su abin da ke faruwa cikin anguwanni da ƙauyuka.

By ukarofi