Kisan mata biyu ya janyo zanga-zanga a ƙauyen Filato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

An shiga fargaba a ƙauyen Gero da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato a ranar Litinin bayan wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun halaka wasu mata guda biyu, lamarin da ya haddasa zanga-zanga daga wasu fusatattun mazauna.

An samu gawar mamatan ne a safiyar ranar a ƙauyen, wanda ke bayan sakatariyar ƙaramar hukumar.

Saidai, ba a samu cikakken bayanin yadda suka riski ajalin nasu ba a lokacin haɗa wannan rahoto.

Al’amarin ya tayar da ƙura acikin mazauna yankin musamman mata da matasa, waɗanda suka ɗauki gawarwakin zuwa sakatariyar domin nuna ɓacin ransu.

Haka kuma, zanga-zangar ta haifar da toshe hanyar da ke kai mutane zuwa sakatariyar, lamarin da ya janyo cinkoson ababen hawa da ɗaiɗaikun mutane.

Wata daga cikin masu gangamin mai suna Misis Mary Chollom, ta bayyana abin alhinin a matsayin tunatarwa game da halin rashin tsaro da ke addabar ƙauyuka da dama a faɗin Filato.

Ta kuma yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin kawo ƙarshen kashe-kashe da babu gaira banu dalili da tabbatar da zaƙulo masu hannu a ciki don su fuskanci hukuncin doka.

Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, ba a samu ji ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alfred Alabo ba akan al’amarin.

By Babaji

Leave a Reply