Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Babbar Kotun Majistare mai lamba 5 da ke Court Road, Kano, ta ba da umarni ga Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano da ya gudanar da bincike kan Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na Kano bisa zargin yin kalaman ɓatanci , tunzuri da kuma maganganun da ka iya haifar da ƙiyayya tsakanin al’umma, musamman a yankin Fagge.
Fitaccen lauya mai rajin kare ƴancin ɗan Adam, Abba Hikima ne ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook.
Ya ce masu shigar da ƙorafin sun haɗa da wasu fitattun malamai, ‘yan kasuwa da shugabannin al’umma, waɗanda suka zargi Abbas da yin maganganu masu cike da raini da tunzuri ga mazauna Fagge.
Kazalika ya ce, an ji Abdullahi Abbas a yayin wani taro yana alakanta mazauna yankin Fagge da rashin tarbiyya da daraja, tare da yin wasu kalamai da suka nuna tsageranci da raina doka, kamar yadda ya saba a lokuta da dama.
