
A ranar Laraba aka gurfanar da waɗanda ake zargin suna wa ƙasar Iran leƙen asiri a Nijeriya
Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta amince da gaggauta sauraron shari’ar wasu mutane uku da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci, ciki har da leken asiri kan ofisoshin jakadancin Amurka da Isra’ila a Najeriya.
Mai shari’a Emeka Nwite ne ya bayar da wannan umarni bayan bukatar da lauyan gwamnati Bello Abu ya gabatar a gaban kotun, wadda kuma lauyoyin wadanda ake tuhuma ba su yi adawa da ita ba.
A zaman kotun, wani jami’in hukumar tsaro ta DSS mai suna James Simon, wanda ya bayyana a matsayin shaida na farko, ya ce daya daga cikin wadanda ake tuhuma, Haruna Ali Abbas, ya amsa cewa an dauke shi aiki domin tattara bayanai kan harkokin Amurka da Isra’ila a Najeriya, musamman ofisoshin jakadancinsu.
Shaidar ta kuma ce Abbas ya bayyana yadda aka horas da su a kasar Iran, inda ya ce wasu sojojin Iran ne suka basu horo kan leken asiri, daukar ma’aikata, tsaron bayanai da kuma sarrafa makamai.
A cewar shaidar, daga cikin ayyukan da aka dora musu akwai tattara bayanai, sa ido da kuma aika sunayen kamfanonin Amurka da Isra’ila da ke Najeriya, tare da bayar da rahotanni kan wuraren da jakadancinsu yake.
Sai dai yayin da ake masa tambayoyi na karkashin bincike, shaidar ya amince cewa bai san takamaiman mutanen da suka horas da su ba, amma ya ce duk wanda ya shiga irin wannan aiki na horar da fararen hula kan amfani da makamai da leken asiri, hakan na iya zama aiki na ta’addanci.
Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 1 ga watan Afrilu domin cigaba da shari’ar.
A wani bangare na zaman kotun, an kuma saurari karar wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a harin da aka kai cocin St Francis da ke Owo a Jihar Ondo a shekarar 2022, inda daya daga cikin wadanda ake tuhuma ya bayyana cewa ba ya iya karatu da rubutu da turanci, kuma hakan ne ya sa ba shi ne ya rubuta bayaninsa da kansa ba.
Wadannan shari’o’i na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro a Najeriya ke ci gaba da kokarin dakile ayyukan ta’addanci da kuma hanyoyin da ake bi wajen yada su a cikin gida da wajen kasar.
