Gwamnan Kano ya sauke Kwamishinan Kasuwanci

Spread the love

Gwamnan Kano ya sauke Alhaji Shehu Wada Sagagi daga mukaminsa na Kwamishinan Kasuwanci da Masana’antu na Jihar.

An rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da daraktan yada labaran gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis 26 ga Maris 2026.

Sanarwar ta ce, an umarci tsohon kwamishinan ya mika ragamar ma’aikatar ga daraktan kasuwanci nan take.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnan ya nuna godiya kan gudunmawar da tsohon kwamishinan ya bayar a lokacin da yake kan mukamin, musamman a fannoni na siyasa da addini da kuma kananan da matsakaitan sana’o’i.

Sanarwar ta kara da cewa matakin na daga cikin gyare-gyare da gwamnatin ke yi domin inganta tafiyar da ayyuka da tabbatar da ci gaba mai dorewa a jihar.

By Babaji