
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya dawo Abuja bayan kammala hutun Sallah karama da kuma ziyarar aiki a ƙasar Birtaniya.
Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce shugaban ya dawo Najeriya da safiyar Juma’a, inda ya halarci sallar Idi a Dodan Barracks da ke Legas.
A lokacin zamansa a Legas, Tinubu ya gana da gwamnoni 23 ciki har da gwamnan Ekiti, Biodun Oyebanji, da kuma attajirin Afirka, Aliko Dangote.
Haka kuma ya karɓi tawagar Tarayyar Turai da mambobin GAC na Legas.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya yi masa bayani kan ziyararsa zuwa Borno bayan harin kunar bakin wake.
Manyan jami’ai da shugabanni ciki har da gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu, be suka raka shugaban zuwa filin jirgi kafin tafiyarsa.
