Daga JOHN D WADA a Keffi
Dr. David Umbugadu, wanda ya kasance ɗan takaran gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Nasarawa, ya sake ficewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai ci a jihar bayan makonni uku kacal da shigowa APC ɗin.
Umbugadu wanda ya tsaya takarar gwamnan Nasarawan a shekarar 2019 da ta 2023, ya tabbatar da murabus nasa ne daga APC a cikin wani wasiƙa ta musamman da ya aika wa shugaban jam’iyyar APC na gundumar sa ta Ika/Wangibi dake ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon a jihar.
Ya bayyana cewa an tursasa shi ne barin sabuwar jam’iyyar na sa ta APC din bayan ya gano wani maƙarƙashiya da ake shirin yi masa don ya rasa kujerar gwamnan jihar a zaɓen 2027 da ke tafe.
Ɗan takarar gwamnan Dr. David Umbugadu daga nan sai ya sake sanar cewa zai koma gidansa na jiya daga APC din wato PDP wanda ya bayyana a matsayin ainihin gidansa na siyasa.
Shi dai sanennen matashin wanda ya daɗe yana neman kujerar gwamnan jihar, Dr. David Umbugadu ya koma APC kwanan nan ne ƙasa da makonni uku kuma an masa gagarumin tarba na musamman a gidan gwamnantin jihar da ke birnin Lafia ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Sule tare da wasu tsofaffin gwamnonin jihar ciki har da Sanata Abdullahi Adamu da wasu masu faɗa-aji na jam’iyyar APC a jihar da ƙasa baki ɗaya da sauran su a ranar 2 ga watan Maris ɗin nan na shekara da ake ciki 2026.
A yanzu dai wasu a jihar na ganin sake komawa gidansa na jiya wato PDP da David Umbugadu yayin ka iya sake canja fasali da kuma tsalon siyasar jihar ta Nasarawa gabanin zaɓen gwamnan na 2027.
