Daga JOHN D WADA a Keffi
Wani Farfesan nazari da jinyar hankali wato professor of Clinical Psychology na fannin karatun rayuwar ɗan-adam (Social Science) a jami’ar jihar Nasarawa, Farfesa Andrew E. Zamani ya bayyana raunin hankali abinda ya kira “Fractured Psyche” a matsayin babbar matsalar dake kawo cikas ga gudanar da shugabanci nagari a nahiyar Afirka baki ɗaya.
Farfesan ya bayyana haka ne a lokacin da yake gudanar da wata lacca ta musamman karo na 58 wanda jami’ar ke shirya wa farfesoshin ta a kowanne wata da aka gudanar jiya Laraba a babban ɗakin taron jami’ar a garin Keffi.
Yace tabbas al’adu da sauran banbance-banbance da dama dake tsakanin al’ummomin Afirka tun zamani aru-aru na mulkin mallaka na turawa a nahiyar Afirka ɗin da yaƙe-yaƙe da gaba da rashin zamantakewa yasa hakan ke cigaba da shafar yanayin shugabanci a yankunan har wa yau.
A cewar Farfesa Andrew Zamani laccar nasa na musamman da yayi wa laƙabi da “Raunin hankalin Afirka da nauyin shugabanci wato “Africa’s Fractured Psyche And the Burden of Leadership” ba yana yi ne don ya ƙasƙanta kima da ilimi ko lafiyar hankali da tunanin ‘yan Afirka ba ne ko wani abu makamancin haka ba, amma yana yi ne don a sake tunani dangane da hakan a kuma nemo mafita cikin gaggawa don tabbatar da cigaba da ingancin tattalin arziki da tabbatar da shugabanci nagari a nahiyar baki ɗaya.
Farfesa Andrew E. Zamani ya kuma bayyana wasu hanyoyin da suka dace da za a iya magance ko samun sauƙin lamarin musamman a ɓangaren shugabanci cewa sun haɗa da sake yin gyarar fuska wa tsare-tsaren hukumomin gwamnatoti a duka matakai da ƙara himmar yaƙan cin hanci da rashawa da tabbatar da gashin kan fannin shari’a wato da inganta fannin ilimi musamman na mata da yara da haɗa kan jama’a da tallafawa matasa da nemo hanyoyin inganta harkokin zuba jari daga ƙasashen waje don bunƙasa tattalin arzikin nahiyar Afirka ɗin da uwa uba tabbatar da cikakken zamani lafiya da sauran su.
Daganan sai ya miƙa godiyarsa na musamman ga shugabar jami’ar ta jihar Nasarawa, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman da duk waɗanda suka halarci laccar inda yace ba shakka idan za a aiwatar da shawarwarin nasa ba Najeriya kaɗai ba nahiyar Afirka baki ɗaya za ta ga canje-canje da dama.
Da take jawabi tun farko, shugabar jami’ar, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman bayan ta yaba wa Farfesa Andrew E. Zamani ta kuma bayyana taken laccar nasa cewa yazo daidai da lokacin nan da nahiyar ta Afirka baki ɗaya ke matuƙar buƙatar farfaɗowa daga doguwar suma da tayi musamman a fannin shugabancin kana ta buƙaci a aiwatar da nazarin Farfesa ba tare da ɓata lokaci ba.
Sauran manyan baki da suka halarci laccar ciki har da sarakunan gargajiya da abokan aiki da ‘yan uwan Farfesa, duk suma sun yaba wa ƙwarewarsa da bajintarsa da kuma gagaruman gudumawa da ya daɗe yana bayar wa cigaban jami’ar da Najeriya da ma Afirka baki ɗaya.
Wakilin mu a jihar ya kuma ruwaito cewa sauran abubuwa da aka gudanar bayan laccar sun haɗa da bai wa Farfesa Andrew Zamani ɗin lambar yabo na musamman daga Farfesa Sa’adatu Hassan Liman inda ta kuma tabbatar da shi a hukumance a matsayin cikakken Farfesa a jami’ar a yanzu da ya gudanar da nashi laccar da ɗaukan hotuna da dauran su.
