
Alƙalin Babbar Kotun Tarayya a Abuja, Joyce Abdulmalik, ta hana ‘yan jarida shiga da kuma ɗaukar rahotan shari’ar wasu mutane shida da ake zargi da shirya juyin mulki.
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan jarida sun isa kotun da sassafe domin bibiyar shari’ar, amma kafin fara zama, jami’an kotu suka umarce su da su fice bisa umarnin alƙaliyar. Duk da ƙorafin da suka yi cewa shari’ar na da muhimmanci ga jama’a, jami’an sun nace cewa umarni ne daga kotu.
Bayan fitar da ‘yan jaridar, an kulle ƙofar kotun, inda daga bisani Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi, ya isa domin halartar shari’ar.
Gwamnatin Tarayya na tuhumar mutane shida da laifuka 13 da suka shafi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Daga cikin waɗanda ake tuhuma akwai Gana, Erasmus Ochegobia Victor (tsohon hafsan ruwa), Ahmed Ibrahim (dan sanda mai aiki), Zekeri Umoru, Bukar Kashim Goni da Abdulkadir Sani.
Kotun ta bayar da umarnin tsare su a hannun DSS tare da fara sauraron shari’ar cikin gaggawa a ranar 27 ga Afrilu.
Haka kuma, an ambaci tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, a cikin tuhumar, amma rahotanni sun ce har yanzu bai shiga hannu ba.
