Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wata Babban Kotu a Katsina ta kori ƙarar da ɓangaren Mustapha Inuwa na jam’iyyar PDP ya shigar inda take ƙalubalantar uwar jami’yyar na jiha da zaɓen shugaban jam’iyyar a matakin kananan hukumomi.
Da ya ke hukunci game da ƙarar, Mai Shari’a Abbas Bawale ya ce kotu ba ta da hurumin shiga harkokin cikin gida na jami’yya.
Ya bada misali da hukuncin Kotun Ƙoli da na Kotun Ɗaukaka ƙara duk akan irin wannan ƙara inda kotunan suka yanke ire-iren waɗannan hukuncin.
Mai Shari’a Bawale ya ƙara da cewa hakan ma biyayya ce ga manyan kotuna saboda haka rikicin cikin gida na zaɓen shugabannin jami’yya matsala ce ta jami’yya bata kai wa kotu ba ta ce.
Ya bada misalai da dama na irin wannan shari’ar tare da kawo sashe-sashe na tsarin mulki na ƙasa da na PDP da suka shafi Shari’a.
To saidai lauyan masu shigar da ƙarar, Barista Mustapha Shittu Mahuta ya faɗa wa manema labarai cewa ya ji daɗin huƙuncin da alƙalin ya yi, ya na mai cewa za su yi nazari a kai kafin ɗaukar mataki na gaba.
Jam’iyyar PDP a Katsina na fama da rikicin cikin gida tsakanin tsagin tsohon Sakataren gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa da Sanata Lado Ɗan-Marke.
