Remi Tinubu ta miƙa ta’aziyya ga gwamnan Jigawa bisa rashe-rashen da aka yi masa

Spread the love

Daga UMAR AKILU MAJERI Dutse

Uwar gidan shugaban ƙasar Nijeriya Olu Remi Tinubu ta jajantawa Gwamna Umar Namadi Bisa rashin mahaifiyarsa Hajiya Maryam A Namadi da babban ɗansa Abdulwahab Umar Namadi da suka rasu a kwanan baya.

Remi ta ziyarci fadar gwamnatin Jihar ne a ranar Asabar tare da tawagarta daga fadar shugaban ƙasa cikin wani yanayi da yake nuna alhini da damuwa a fuskarta bisa rashin da a ka yiwa gwamnan jihar ta Jigawa da al,ummar Jihar baki ɗaya a kwanan baya .

Remi a cikin bayananta tace dukkan mai rai mamaci ne kuma kowa ita yake jira wato mutuwa ,sai dai tayi fatan Allah yasa muyi kyaukyawan ƙarshe.

Tace a lokacin da ta Sami labarin rasuwar mahafiyar gwamnan ba ta Nijeriya ta fita waje wata ziyara, kuma washe gari ta sake samun labarin rasuwar babban yaronsa, lamarin ya yi matuƙar tada mata hankali sosai.

Remi tace irin wannan rashi ba ƙaramin al amari ba ne ga duk wanda ya shafa.

Ta ƙara da cewa haka yasa daga dawowar ta gida babu abinda ta yi shine ta garzayo nan Jihar Jigawa domin ta gabatar da ta’aziyya ga gwamnan jihar da iyalansa da duk al,ummar Jihar Jigawa gaba ɗaya.

A karshe ta yi fatan Allah ya yafewa Hajiya Maryam A Namadi dukkan laifukan da ta aikata zamanin ta na raye, ya kuma gafarta wa jikanta Abdulwahab Umar Namadi, ya sa aljanna makoma a garesu .

Da ya ke mayar da jawabi gwamna Umar Namadi ya godewa uwar gidan shugaban ƙasa Olu Remi Tinubu bisa kulawa da damuwarta da ta nuna game da rashin ɗansa da kuma rashin mahaifiyar sa.

Namadi ya cigaba da cewar dama ita mutuwa haka take, tana faruwa akan kowa duk wanda lokacin sa ya yi ba makawa dole sai ya tafi, kuma dukkanmu zamu mutu domin ita muke jira, su ma da su ka koma ga Allah ba sun mutune ba domin Allah baya son su ba,sai dai lokacin su ne yayi kuma Allah Yana buƙatar su shine ya ɗauke su.

Saboda haka yayi addu’ar allah ya kai rahama kabarin su ya yi ma su sakamako da gidan Aljanna Firdausi.

By ukarofi