Gwamnatin Kano ta bai wa ɗan bijilantin da ƴan daba suka raunata tallafin N500,000

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta tallafa wa matashi Musa Muhammad Kallah dake aikin bijilanti da ƴan daba suka farmaka da kuɗi har naira dubu dari biyar don cigaba da kula da lafiyarsa.

Da ya ke miƙa kuɗin, wakilin Gwamna Abba Kabir Yusuf, Babban daraktan ayyuka na musamman kuma mai kula da ɓangaren harkokin jami’an tsaro AVM Ibrahim Umaru (RTD) ya bayyana irin halin da mai girma gwamna ya tsinci kansa yayin da labarin ya same shi.

Babban Daraktan ya ce ƙoƙarin mai girma gwamna ne na tausaya tare da nuna damuwa ga dukkan wani mutum da ya fuskanci matsala a jihar Kano.

”Kamar yadda kuka sani yau mai girma gwamna ya turo ni da tawaga ta domin duba wannan bawan Allah da wannan matsala ta faru da shi dan jajanta mashi tare da ba shi tallafin kudin nan da kuka gani.”

Gwamnan ya kuma tabbatar wa matashin cewa gwamnati za ta cigaba da kula dashi har lokacin da zai samu lafiya ya koma bakin aiki.

”Da wannan muke kira ga masu hannu da shunin da ke zaune a anguwar Ɗorayi da su tashi tsaye wajen ƙara taimaka wa gwamnati kan ƙoƙarinta na samar da zaman lafiya da taimakon al’umma.

AVM ya kuma kara da cewa gwamnati na kara godiya ga bakin daukacin kungiyar matasan Dorayi bisa ƙoƙarin da suke wajen ganin sun samar da kwanciyar hankali.

A nasa jawabin, Musa Muhammad Kallah ya nuna godiyarsa ga gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba bisa ƙoƙarin da ya yi na tallafin.

By ukarofi