Masu dukan mata ku tuba ku daina

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kwanaki wata marubuciya ta yi wani rubutu a shafinta na Facebook, inda ta bayyana takaicinta game da halayyar wasu azzaluman maza da ke cin zarafin matansu ta hanyar duka, abin da ya jawo muhawara mai zafi daga ɓangarori daban-daban, sakamakon yadda wannan mummunar halayya ke ci musu tuwo a ƙwarya.

Mata da dama, musamman masu aure, suna kokawa da yadda wasu mazan ke kasa daurewa fushi da ɓacin ransu, da zarar matansu sun musu wani kuskure ko laifi sai su hau jibgarsu kamar jakuna, ba mutane ba. Wani lokaci ma idan abin ya zo da tsautsayi har lahani ake ji musu, a jikkata su kamar targaɗe ko karaya a wani sashi na jikinsu, idan ma abin ya zo da ƙarar kwana har kisan kai ake yi.

Kofi Anan, tsohon Babban Sakataren Majalisar ɗinkin Duniya, ya taɓa bayyanawa a cikin wani rahoton 2006 da aka buga a shafin Asusun Inganta Rayuwar Mata na Majalisar ɗinkin Duniya (UNIFEM) cewa, ‘Cin zarafi ga mata da ‘yammata matsala ce babba da ta addabi duniya. Aƙalla ɗaya daga cikin mata uku a duniya ana yi musu dukan tsiya, da tilasta musu yin jima’i, ko kuma a ci zarafinsu ta hanyar faɗa musu wasu kalamai na ɓatanci da muzantawa, daga makusantansu, kamar ’yan’uwa ko mazajensu na aure.’

Cin zarafin mata wanda aka fi sani da cin zarafin jinsi ayyuka ne na rashin kyautatawa masu ɗaga hankalin duk wani mutum mai tunani da sanin ya kamata. Ana ɗaukar irin wannan halayya ta mugunta da cin zali a matsayin wani nau’i na nuna wa jinsin ‘ya mace ƙiyayya, kuma yana iya ɗaukar wasu nau’uka daban-daban.

A nan Nijeriya, bincike ya nuna cewa kashi 19 cikin ɗari na cin zarafin da ake yi wa mata na da nasaba ne da tauye haƙƙoƙi da wulaƙanci. Yayin da kashi 14 cikin ɗari ya shafi lahantawa ta fuskar duka ko illata wani ɓangare na jiki. Sannan sai matan da ake yi wa fyaɗe da wani nau’i na cin zarafi ta hanyar jima’i, kamar ’yan mata ko ƙananan yara mata, ba su wuce kashi 5 cikin ɗari ba. Wannan ga waɗanda a hukumance ake da ƙiyasinsu kenan, ban da waɗanda ba a sanar da hukumar ’yan sanda ko wata cibiya da ke nazari da ɗaukar abin da muhimmanci cikin ayyukanta ba. A lokuta da dama iyaye ko ’yan uwa kan yi ƙoƙarin ɓoye maganar rashin mutuncin da ake nunawa ‘yarsu ko cin zarafin da aka yi mata, don kaucewa zubewar mutuncinta a idanun al’umma. 

Marubuciyar da na fara buɗe wannan sharhi da bayani kan rubutun da ta yi, ta ba da labarin wata matashiyar mata mai da ta gani a wani gida tana ta faman kuka, cikin wani yanayi marar daɗi, ta bayyana cewa sai da lallashi ta samu matar ta yi shiru sannan ta tambayeta abin da ke damunta. 

“Mijina ne kullum sai ya dake ni. Ko da akwai taimakon da za ki iya yi min?” Amsa da tambaya duk a lokaci ɗaya, cikin tausayi na ce mata, “To, ke ina iyayenki, ko iyayen mijinki? Me ya sa ba za ki sanar da su abinda ke faruwa ba?” Sai ta ce, “Ai na sha faɗa musu amma babu wani mataki da aka taɓa ɗauka, sai ma aka dinga cewa ƙarya nake masa. Mahaifina bai taɓa yarda da ni ba, ko na je ma koro ni yake yi.” Wannan ita ce amsar da wannan mata ta bai wa marubuciyar.

Gaskiya bai kamata a ce iyaye su riƙa yin kunnen uwar shegu da kukan da ’yarsu ke kawo wa gida ba, musamman idan ya shafi cin zarafi ko muzantawa, don gudun kar a yi ɗa kwance uwa kwance. Domin a ƙarshe idan abin ya zo da tsautsayi, zai iya illata musu ’ya ko ’yar uwa kuma ya rabu da ita, bayan ya lalata mata rayuwa, in ma bai hallaka ta ba kenan. 

Akwai wani labari ma na wata amarya da aka ce ko wata biyu ba su yi da aure ba, amma har mijin ya fara lakaɗa mata duka. Amma abin mamaki ta kasa yarda kowa ya san zancen tsakanin maƙwafta da iyayenta. Abin da ya sa wasu zargin ko dai laifin nata ne ya sa ta kasa kai ƙara don a tsawatarwa sabon angon nata. Duk da kasancewar wasu na nuna cewar tsananin son da mace ke yi wa mijinta yana sa ta ɓoye laifinsa, don kar wani abu ya sa a raba su. Tunda an ce, so hana ganin laifi!

Kodayake duk da rashin hankalin da wasu maza ke nunawa na rashin riƙe matansu da mutunci da kyautatawa, akwai wasu matan da ke ganin idan mazajensu ba sa dukansu kamar ba su damu da su ba ne, ko kuma ba sa nuna kishi a kansu. Don haka ne ma duk runtsi za ka same su a ɗakin aurensu suna haƙuri da halin da suke ciki.

Na taɓa samun labarin wata mata da ta gaji da dukan da mijinta ke yi mata a kullum, ita ma ta juya kansa, har ta illata shi sosai ta yadda aka ce tun daga ranar bai sake kai hannu jikinta da niyyar duka ba. Wata kuma ita da mijin suka zama kamar ’yan daba, idan yau wannan ya jikkata wancan, sai kuma gobe wancan ya rufa a kan wannan, wanda ya nakasa ɗan uwansa sai ya kai shi asibiti, in sun huta a cigaba daga inda aka tsaya. Tun ’yan’uwa da maƙwafta na sa baki don a sasanta lamarin, har dai kowa ya haƙura ya sa musu ido, tunda sun kasa bari kuma sun kasa rabuwa. Subhanallah!

Ba tun yanzu ba mata da dama a duniya ke fuskantar irin wannan mummunar halayya bisa dalilai na al’ada ko addini, ko kuma nuna fin ƙarfi daga ɗabi’ar wasu mazan. Na ce wasu ne don na san ba duka ne aka taru aka zama ɗaya ba. Akwai maza da dama da ba sa iya ɗaga hannu su mari matansu, ballantana duka ko jikkatawa. Suna kuma kula da haƙƙoƙin matansu, kare mutuncinsu da yabawa ƙoƙarinsu. Kodayake wasu masana na danganta abubuwan da suke sa wasu maza yawan zafin rai da saurin kai hannu da zarar an ɓata musu rai, na da nasaba da yanayin rayuwar da suka taso a ciki. Abin nufi, idan sun tashi cikin iyalin da ake samun yawan faɗace-faɗace a tsakanin iyali, ko kuma uba yana dukan babarsa a kan idanunsa, ko ya gamu da wani mugun uba da ba ya saurara masa da zarar ya yi laifi. To, hakan yana sa yaro ya tashi da tsananin ƙunci a zuciyarsa, kuma ya riƙa ƙoƙarin ganin ya rama muguntar da aka yi masa, ko kwatanta abin da babansa yake yi wa babarsa, a kan matarsa. 

Sau da yawa ana ganin masu irin wannan halayya ta dukan mata a matsayin lalatattun mutane, marasa natsuwa da imani. Don idan ka lura za ka ga akasari maza masu wulaƙanta mata su ma ba martaba ko kima suke da ita a cikin mutane ba, wani lokaci ma sai sun yi shaye-shayensu, sun fita a hayyacinsu kafin su aikata haka a kan matansu. 

Duk da dokokin da gwamnati ke sa wa a matakin tarayya da na jihohi domin kawo ƙarshen cin zarafin mata da wulaƙancin da ake nuna musu, har yanzu irin wannan halayya tana cigaba, musamman a ƙauyuka da maraya. Jihohi da dama a Nijeriya sun sanya hannu a wata doka da ake kira da suna, ‘Dokar Haramta Cin Zarafin ɗan Adam’, a turance ana mata laƙabi da ɓiolence Against Persons Prohibition Act (VAPPA). A ƙarƙashin wannan doka ne ake hukunta duk wani azzalumi da ke tauye haƙƙoƙin wani ko wasu, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya basu. Sannan akwai dokar da ta take yaƙi da cin zarafin yara mata, ko kuma ƙananan yara mata da ake yi musu auren dole ko yi musu fyaɗe da sauran nau’ika na cin zarafi. Wannan doka ana ce mata, ‘Dokar Kare Haƙƙoƙin Yara’, wato da turanci, ‘Child Rights Act’ kenan. 

Lallai ne ma’aurata su sani gidan aure ba gidan dambe ba ne. Kuma mace ita ma mutum ce mai mutunci da daraja kamar kowanne ɗan adam. Tauye haƙƙin mace a gidan aure da wajensa babban laifi ne a dokar ƙasa da ta duniya, wanda idan aka gurfanar da mutum a gaban shari’a zai iya fuskantar hukunci mai tsanani ko tara. 

Babu inda jin daɗi da farinciki ke samuwa a rayuwar aure idan babu nuna wa juna soyayya da kyautatawa, idan babu tausayi da rarrashi, ko idan babu ladabi da biyayya.