Daga AISHA ASAS
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta kama wani mai fasahar zance, Emeka Emmanuel Mbadiwe da laifin safarar kashi 33 na Loud, wato tabar wiwi mai nauyin kilogiram 17.30.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai da bayar da shawarwari na hukumar Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi.
A cewar Babafemi, Mbadiwe, wanda kuma ɗan wasan finafinan Hollywood da na Nollywood ne da Amurka ta horar, an kama shi ne a ɗakinsa na otal ɗin Lekki ranar Juma’a 27 ga watan Disamba, 2024, biyo bayan kama abokin aikinsa, Uzoekwe Ugochukwu James, da safiyar ranar a wani ɗakin ajiyar kaya da ke Estate Ajao, Ikeja, inda Mista Mbadiwe ya aike shi ya karɓo tabar ta wiwi mai nauyin 17.30 kilogiram. Wadda ta iso a ɓangaren shigo da kaya na filin jirgin sama na Murtala Muhammed
Jirgin da ya ɗauko tabar dai ya isa babban ɗakin shigo da kaya na filin jirgin saman Murtala Muhammed, MMIA Ikeja a ranar 24 ga watan Disamba, 2024 daga ƙasar Amurka, kuma ɗaya ne daga cikin jiragen Delta Airline, wanda aka shigo da ita a boye, cikin manyan akwatunan katako.
Har ila yau, sanarwar ta bayyana cewa, hukumar ta kama wata gawurtacciyar ‘yar safarar ƙwayoyi da ake nema ruwa a jallo, mai suna Alhaja Aishat Feyisara Ajoke Elediye mai shekaru 61 a duniya.
An kama Elediye ne a ranar Laraba, 1 ga watan Junairu, 2025, a gidanta da ke unguwar Okota a Legas, biyo bayan kama wata babbar mota ɗauke da miyagun ƙwayoyi daga hannun ma’aikatanta a ranar.
A cewar sanarwar, a ranar 1 ga Janairu, 2025, jami’an NDLEA sun kama wata mata mai suna Alhaja Aishat Feyisara Ajoke Elediye, mai shekaru 61, wacce aka fi sani da “Iya Ruka,” a gidanta da ke Okota, Legas.
Ta kasance cikin jerin sunayen da hukumar ke nema ruwa a jallo, sakamakon jagorantar wata babbar ƙungiyar masu safarar miyagun kwayoyi a Mushin da take yi.
Sanarwar ta ce, “Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta fara sabuwar shekara da kama wata jagorar masu safarar miyagun ƙwayoyi da ake nema ruwa a jallo, mai suna Alhaja Aishat Feyisara Ajoke Elediye, mai shekaru 61 a duniya, a ranar Laraba, 1 ga Janairu, 2025. A gidanta da ke Okota, Legas, biyo bayan kama wata babbar mota ɗauke da miyagun ƙwayoyi da ma’aikatanta suka yi a ranar.
“Wadda aka fi sani da ‘lya Ruka’, Alhaja Ajoke, kamar yadda ake kiran ta a duniyar safarar ƙwayoyi, sunanta ya yi ƙauren suna tsayin shekaru, yayin da ta ci gaba da kasancewa cikin jerin waɗanda NDLEA ke nema ruwa a jallo domin jagorantar ɗaya daga cikin masu safarar miyagun ƙwayoyi, a unguwar Mushin da ke Legas.
“kamen ya samo asali ne daga ranar Laraba 1 ga watan Janairu, 2025, lokacin da jami’an NDLEA da ke aikin leƙen asiri, suka kama wata farar motar Izuzu da ke ɗauke da buhu 44 da aka cika da tabar wiwi wadda aka shigo da kilogiram 1,540, inda ɗaya daga cikin ma’aikatanta, Abideen mai shekaru 41 ya tuƙa. Daga nan ne ‘yan sandan suka kai farmaki maɓoyar ta mai lamba 33 Adebayo Oyewole, kusa da fadar Ago Way, Okota, inda suka kama ta.
“A zahiri, Alhaja Ajoke ‘yar kasuwa ce da ke shigo da yadudduka da takalma daga ƙasar Sin, amma a ƙarkashin ƙasa akwai haramtacciyar fataucin miyagun ƙwayoyi da take yi. An kuma san ta a matsayin lyalaje ta Blessing Sisters, wata babbar ƙungiyar cigaban mata mai tasiri a cikin al’ummar Legas.”
Sanarwar ta ƙara da cewa, “A wani gagarumin farmaki da jami’an NDLEA suka yi a ranar Juma’a, 27 ga watan Disamba, 2024, sun kama wani mai shirya finafinan Hollywood da na Nollywood Emeka Emmanuel Mbadiwe, wanda kuma mai azancin magana ne na ƙarfafa gwiwa, a ɗakinsa na otal na Lekki bayan kama abokin aikinsa, Uzoekwe Ugochukwu James, a wani sito da ke Ajao Estate, Ikeja. James ya aike da Mbadiwe domin ya karɓo kaya na Loud guda 33. Wani nau’in tabar wiwi mai nauyin kilogiram 17.30, wanda ya isa wurin shigo da kaya na filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA) Ikeja a ranar 24 ga Disamba 2024, inda aka ɓoye ta a manyan akwatunan katako.
A Ilorin, jami’an NDLEA sun kama Khadijat Abdulraheem ‘yar shekara 24 da kuma Ayomide Morakinyo ‘yar shekara 20 a ranar 29 ga Disamba, 2024, bisa laifin siyar da kek da suke yi mai ɗauke da miyagun ƙwayoyi a ciki ga ɗalibai. A wani bincike da aka gudanar a ɗakin kwanansu, an samu kek 42 da ke ɗauke da ƙwaya a cikinsa.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “A Jihar Kwara, jami’an NDLEA sun kama wata matashiya da ba ta jima da kammala karatun digiri ba, Khadijat Abdulraheem, ‘yar shekara 24, da kuma ‘yar shekara 20, Ayomide Morakinyo na Jami’ar Ilorin a ranar Lahadi, 29 ga Disamba, 2024, bayan samun su da laifin saidawa ɗalibai kek mai ɗauke da ƙwaya.”
