Kotu ta mayar wa Ali Musa kujerar takarar shugabancin Kumbotso a Kano

Spread the love

Daga RABI’U SANUSI

Ana tsaka da yanke hukunci a babbar kotun jiha mai lamba huɗu ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Usman Na Abba sai jam’iyyar NNPP ta mazabar Ɗan Maliki da ke cikin ƙaramar hukumar kumbotso ta fitar da sanarwar ta kori Hon Ali Musa hard worker daga jam’iyyar NNPP.

Kotun kuma ta tabbatar da Hon Ali Musa Ɗan Maliki a matsayin halastaccen ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar kumbotso ƙarƙashin tutar jam’iyyar NNPP.

Tun a baya dai majiyar mu ta ruwaito cewar, jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya janye sunan Ali Musa hard worker a matsayin ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukumar Kumbotso ya maye gurbin sa da Hon Ghali Basaf a matsayin shi ne wanda zai yiwa jam’iyyar takarar shugabancin karamar hukumar Kumbotso ƙarƙashin tutar jam’iyyar NNPP.

Inda a wannan rana babbar kotun jiha ta tabbatar da Hon Ali Musa Dan Maliki(Hard worker) a matsayin halastaccen ɗan takarar shugabancin karamar hukumar Kumbotso ƙarƙashin tutar jam’iyyar NNPP.

Yanke hukuncin ya biyo bayan wasu ƙwararan hujjoji da lauyan Ali Musa, Barr Jazuli Mustapha ya shigar gaban kotun, inda kuma lauyan jam’iyyar NNPP da na KANSIEC suka gaza bayar da hujja ko guda da za ta ƙalubalanci hujjojin Barr Jazuli Mustapha.

By ukarofi