
Wata Kotun Shari’a da ke Kano ta umarci Hukumar Hisbah ta jihar da ta shirya ɗaura aure tsakanin wasu fitattun ’yan TikTok guda biyu, wato Idris Mai Wushirya da Basira ‘Yar Guda acikin kwanaki 60.
Kotun ta bada umarnin ne bayan yaɗuwar bidiyon mutanen biyu a kafafen sada zumunta, da Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bayyana a matsayin ‘batsa da rahsin tarbiyya’ acikin al’umma.
Bidiyoyin sun nuna yadda ’yan TikTok ɗin suka nuna soyayya a bainar jama’a, lamarin da hukumomi suka ce ya saɓa wa ɗabi’u da koyarwar addini da al’adun mutanen Jihar Kano.
A yayin zaman kotun ranar Litinin, Mai Shari’a Halima Wali ta yi gargaɗi cewa idan ba a ɗaura auren cikin lokacin da kotun ta ƙayyade ba, za a ɗauki hakan a matsayin raina kotu.
Kotun ta kuma umurci Shugaban Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano Jihar Kano da ya tabbatar da aiwatar da wannan umarni na aure.
A makonnin baya an gurfanar da Mai Wushirwa da ’Yar Guda a gaban kotu bisa zargin yi da kuma yaɗa bidiyoyi masu nuna abin da aka bayyana a matsayin “batsa ko rashin kunya” a kafafen sada zumunta.
Tun da farko sai da kotu ta tura Mai Wushirya gidan yari saboda ɓullar wasu bidiyoyi da suka nuna shi yana aikata abin da hukumomi suka kira “aikata rashin kunya da tauye darajar addini” tare da yarinyar abokiyar aikinsa.
Hukumar tace fina-finai ta jaddada cewa waɗannan bidiyoyi sun karya dokokin jihar da ke haramta samarwa da yaɗa abubuwan da ke da alamar batsa ko rashin kunya.
