
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an rundunar ƴan sanda a Abuja, sun kama ɗan gwagwarmaya kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore.
A yau Alhamis aka kama shi jim-kaɗan da fitowarsa daga Babbar Kotun Tarayya.
ShaharaReporters ta ruwaito cewa kwamishinan ƴan sandan Abuja ne ya umarci a kama ɗan gwagwarmayar.
Sowore, wanda aka tsara zai gurfana a gaban Mai Shari’a Emeka Nwita bisa abin da ya wassafa a matsayin cajin “ƙarya da dangogi” na ‘yan sanda wanda “haramtaccen Sufeto Janar, Kayode Egbetokun”, an sanar da shi alƙalin ba zai zauna ba.
Wata majiya ta ce, an shaida wa Sowore cewa an kama shi ne bisa umarnin Kwamishinan ƴan sandan Abuja.
A yayin haka ne tawagar shari’arsa ƙarƙashin jagorancin Tope Temokun suka nemi ji ta bakin ƴan sandan domin jin dalilin kamen, inda suka bada amsa da cewa umartar su aka yi.
