Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kotun ƙoli ta Tarayya da ke Abuja ta bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu umarni ya tura wa Babban Lauyan ƙasa umarnin gaggawa domin bayyana sunayen dukkan mutanen da kamfanonin da aka gano su na da hannu a zambar kuɗi sama da Naira Tiriliyan shida da aka ware wa Hukumar Ci gaban Yankin Neja-Delta (NDDC) tsakanin shekarun 2000 zuwa 2019.
Wannan hukunci, wanda mai shari’a Gladys Olotu ta yanke a ranar Litinin 10 ga Nuwamba, ya samo asali ne daga ƙarar FOI da ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙinda cin hanci da rahswa ta shigar tun Nuwamba 2021, domin tilasta gwamnati ta bayyana cikakken rahoton binciken kwakwaf na NDDC.
Rahoton dai an miƙa shi ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari tun ranar 2 ga Satumba 2021, amma har tsawon shekaru huɗu babu amsa.
A hukuncin ta, Justice Olotu ta bayyana cewa rahoton kwakwaf ɗin da sunayen waɗanda aka kama da laifi “muƙaman takardu ne na jama’a” a ƙarƙashin Sashe na 31 na Dokar FOI, wanda hakan ya haramta ɓoye su.
Ta ƙara da cewa, bayanan da SERAP ta nema ba su cikin abin da dokar ta ware a sassan 11 zuwa 19 — don haka gwamnati ba ta da hujjar ƙin bayyana su.
Mai shari’ar ta yi nuni da cewa ƙin bayyana rahoton bayan an yi rubutacciyar buƙata daga SERAP ya zama keta dokar FOI da kuma Sashi na 15(5) na Kundin Tsarin Mulki na 1999, wanda ya wajabta kare amanar jama’a da tabbatar da gaskiya a harkokin kuɗi.
Ta jaddada cewa FOI ba dokar zaɓi ba ce—dole ne duk wata ma’aikatar gwamnati ta bayyana bayanan da suka shafi kuɗin jama’a idan an nema.
Mataimakin Daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya bayyana hukuncin a matsayin “nasara mai tarihi ga gaskiya da adalci,” yana mai cewa lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya su san yadda tiriliyan da aka ware na ci gaban Neja-Delta suka ɓace ba tare da alamar amfani ba.
Ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya bi hukuncin nan take domin kare martabar gwamnatinsa.
Femi Falana, SAN, ya yaba wa kotun, yana kiran hukuncin “ɗaya daga cikin shari’o’in da suka fi kishin ƙasa tun farkon yaƙin da cin hanci.” Ya yi gargaɗin cewa kin bin hukuncin zai raunana yaƙi da cin hanci ya kuma rage wa gwamnati kima a idon jama’a.
SERAP ta riga ta rubuta wa Shugaba Tinubu wasiƙa a ranar 22 ga Nuwamba 2025, tana neman ganin an aiwatar da hukuncin ba tare da ɓata lokaci ba.
A cewar ƙungiyar, bayyana sakamakon rahoton da sunayen waɗanda suka aikata laifuka zai cika burin jama’a, ya kuma nuna cewa gwamnatin Tinubu na da jajircewa wajen inganta gaskiya, adalci da bin doka — ginshiƙan manyan sauye-sauyen da ta saba faɗa a bainar jama’a.
Daga 2000 zuwa 2019, an ware wa NDDC kimanin naira tiriliyan shida domin ayyukan gine-gine a faɗin Neja-Delta. Amma bincike daban-daban ya nuna cewa yankin bai ga canji sosai ba, kasancewar an riƙa ambaton ɓarnar kwangiloli, tsangwamar siyasa, ayyuka masu cikas da kuma karkatar da kuɗaɗen jama’a — lamarin da ya sa aka gudanar da wannan bincike na musamman tun 2019. Sai dai duk da girman tattaunawar jama’a, rahoton ya zauna a duhu har zuwa hukuncin da aka yanke yanzu.
