Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Birtaniya ta ƙi amincewa da buƙatar da gwamnatin Nijeriya ta gabatar mata na dawo da Ike Ekweremadu gidan yari a Nijeriya domin ya ƙarasa wa’adinsa.
Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ƙasar na zaman kaso ne a Birtaniya bayan kama shi da laifin safarar sassan jikin bil’adama.
An yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 9 da wata takwas a watan Maris ɗin 2023, saboda kitsa yadda za a cire ƙodar wani matashi domin a dasa wa ’yarsa Sonia da ke fama da ciwon ƙoda.
A watan Nuwamba ne shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da wata babbar tawaga birnin Landan domin tattauna hukuncin da aka yanke masa, da kuma duba yiwuwar dawo da shi Nijeriya ya ƙarasa wa’adinsa.
