Yadda Jonathan ya tsallake rijiya da baya a juyin mulkin Guinea-Bissau

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta tabbatar da cewa, Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Ebele Jonathan, yana cikin ƙoshin lafiya kuma ya samu nasarar ficewa daga ƙasar Guinea-Bissau bayan juyin mulkin soja da ya girgiza ƙasar a lokacin da Jonathan ɗin ke cikin ƙasar.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa, ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya.

A cewarsa, “Tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan yana cikin ƙoshin lafiya, kuma tuni ya fice daga Guinea-Bissau ta jirgin musamman tare da mambobin tawagarsa ciki har da Mohamed Chambas.”

Jonathan ya kasance a Guinea-Bissau ne a matsayinsa na shugaban Kwamitin Dattawan Afirka ta Yamma na sa ido kan zaɓe, lokacin da sojoji suka sanar da ƙwace ikon mulkin ƙasar, suka rufe iyakoki tare da karɓe manyan hukumomin gwamnati bayan zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar dokoki da aka gudanar ranar Lahadi.

A wata sanarwa ta haɗin gwiwa da aka fitar ranar Laraba, Jonathan tare da tsohon Shugaban ƙasar Mozambiƙue, Filipe Nyusi, da kuma shugaban tawagar sa-ido na ECOWAS, Issifu Kamara, sun yi Allah wadai da juyin mulkin, suna mai bayyana shi a matsayin mummunan hari kan dimukraɗiyyar Guinea-Bissau.

Sun kuma buƙaci al’ummar ƙasar da su kwantar da hankulansu tare da jaddada ƙudirinsu na ci gaba da tallafa wa ƙasar domin kare zaman lafiya, kwanciyar hankali da rayukan jama’a.

Haka kuma, Gwamnatin Tarayya ta Nieriya ta yi kakkausar suka ga juyin mulkin, tana mai bayyana shi a matsayin babbar barazana ga dimokuraɗiyya da zaman lafiyar yankin Afirka ta Yamma.

Ma’aikatar Harkokin Waje ta ce ta karɓi labarin kifar da gwamnati da “matuƙar alhini da damuwa mai tsanani,” tana mai jaddada cewa hakan ya saɓa wa ƙa’idojin dimokuraɗiyya na ECOWAS.

Guinea-Bissau ta faɗa cikin ruɗani a ranar Laraba bayan wasu manyan jami’an soja sun sanar da karɓe cikakken iko da ƙasar, suka rufe iyakoki, suka dakatar da dukkan al’amuran zaɓe, tare da jibge sojoji a manyan tituna da muhimman wurare a birnin Bissau. Rahotanni sun ce an ji ƙarar harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya ƙara jefa jama’a cikin fargaba.

Shugaban ofishin tsaron shugaban ƙasa, Denis N’Canha, ya sanar da cewa wani kwamitin soja da ya ƙunshi dukkan ɓangarorin rundunar tsaro ne ya karɓi jagorancin ƙasar na wucin gadi.

A wata hira ta wayar tarho da tashar France24, Shugaban ƙasar da aka kifar, Umaro Sissoco Embalo, ya tabbatar da cewa an sauke shi daga mulki, inda rahoton AFP ya ce yana fakewa ne a hedikwatar soji tare da shugaban hafsoshin tsaro da ministan cikin gida.

By ukarofi