’Yan sanda 11,566 sun janye wa manyan mutane bayan umarnin Tinubu 

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Umarnin da Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya bayar na rage yawan ’yan sandan da ke gadin manyan mutane ya fara aiki, bayan da Babban Sufeton ’Yan Sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa, an janye jami’ai 11,566 daga ayyukan gadin manyan mutane tare da mayar da su manyan ayyukan tsaro a faɗin ƙasa.

Egbetokun ya bayyana hakan ne a yayin taro da manyan kwamandojin ’yan sanda a Abuja a ranar Alhamis, inda ya ce matakin wani shiri ne na musamman da aka ƙaddamar domin ƙarfafa aikin tsaro a sahun gaba da dawo da ganin ’yan sanda a unguwanni da garuruwan da ke fuskantar barazanar tsaro.

Ya ce, jagorancin rundunar ’yan sanda ya goyi bayan matakin ɗari bisa ɗari, yana mai bayyana shi a matsayin gyaran kuskuren shekaru da dama, sakamakon yawan daƙile jami’ai wajen bada tsaro ga manyan mutane fiye da kima.

A cewarsa, “Dangane da umarnin Shugaban Kasa, mun janye jami’an tsaro 11,566 da ke gadin manyan mutane, kuma tuni aka fara mayar da su muhimman ayyukan tsaro a faɗin ƙasa.”

Babban sufeton ya bayyana cewa wannan mataki zai ƙara yawan jami’an da za su riƙa gudanar da sintiri a karkara da birane, da ayyukan leƙen asiri, da gaggawar kai ɗauki, da kuma kare yankunan da ke fuskantar barazanar ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran manyan laifuffuka.

Egbetokun ya jaddada cewa janyewar ba ta da alaƙa da hukunci ko son rai, sai dai wani yunƙuri ne na sake tsugunar da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya kan madaidaicin tafarkin aikinta.

“Wannan janyewa ba ja da baya ba ne daga nauyin da muke ɗauke da shi, illa dai dawo da nauyin zuwa inda ya dace,” inji shi.

Ya ce, nan ba da jimawa ba rundunar za ta fitar da cikakkun ƙaidoji kan yadda za a aiwatar da wannan tsari, domin hana damfara, yaudarar jama’a ko aikata laifi da sunan wasu jami’an tsaro na bogi.

Babban sufeton ya kuma yi ishara da wasu sabbin al’amuran rashin tsaro da suka haɗa da sace mutane a jihohin Kwara, Kebbi da Neja, al’amuran da suka jawo hankalin jama’a kan rawar da ’yan sanda ke takawa.

“Ko da ba mu yi yadda ake so ba a wasu lokuta, ba yana nufin ba mu aiki ba ne. Muna aiki tuƙuru, amma a matsayinnmu na shugabanni, wajibi ne mu riƙa ɗaura wa kanmu nauyi mafi girma,” inji shi.

Egbetokun ya bayyana cewa cikin ’yan makonnin nan kaɗai, rundunar ta samu manyan nasarori da suka haɗa da kama mutane 8,202 kan laifuffuka daban-daban, ciki har da fashi da makami, garkuwa da mutum, kisan kai, mallakar bindiga ba bisa ƙa’ida ba, fyaɗe da ayyukan ƙungiyar asiri. Haka kuma an ceto mutane 232 da aka sace, an kwato bindigogi da dubban harsasai da kuma motoci da aka sace.

Ya ƙara da cewa, rundunar na ƙara ƙaimi wajen hulɗa da al’umma, tattara bayanan sirri da ƙarfafa gwiwar haɗin guiwa da sauran hukumomin tsaro domin daƙile ayyukan ta’addanci.

Tare da ƙaruwar zirga-zirgar mutane a watan Disamba, Egbetokun ya umurci dukkan rundunonin jihohi da su ƙaddamar da tsare-tsaren tsaro na warshen shekara, tare da ƙarfafa sintiri, sa ido da ayyukan tsaron hanya.

“Masu laifi za su yi ƙoƙarin cin moriyar hanyoyi, saboda haka wajibi ne a mamaye hanyoyin baki ɗaya da tsaro mai zurfi da shiri mai ƙarfi,” inji Babban Sufeton.

By ukarofi