Daliban Maga: An tada jijiyar wuya tsakanin Gwamna Idris da Sanata Maidoki

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Bayan sace ɗaliban ‘yan matan makarantar GGCSS Maga a ranar Litinin 17 ga watan Nuwambar nan an tada jijiyoyin wuya tare da nuna yatsa tsakanin gwamnatin jihar Kebbi da kuma ɗan majalisar dattawa Sanata Garba Maidoki mai wakiltar gundumar Kebbi ta Kudu wanda daman dangatakarsu tana da tsami kafin wannan lokacin.

Taƙaddamar dai ta soma ne bayan da Gwamna Malam Nasir Idris tare da gwamnatin tarayya suka sha alwashin gano musabbabin ɗagawar jami’an tsaro da aka girke a makarantar domin bai wa ɗaliban kariya bayan samun bayanan sirri na cewa akwai yiyuwar kawo farmaki a makarantar.

Wani mai magana da yawun waɗanda suka yi garkuwa da ɗaliban a wani faifan bidiyo ya bayyana cewa sace ɗaliban ya biyo bayan wani cika-baki ne gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya yi a kwanan baya inda ya ke cewa babu sansanin ‘yan ta’adda ko ɗaya duk faɗin jihar Kebbi ballantana masu ta’addaci wannan yana ɗaya daga ciki.

Ya kuma bayyana cewa sun tabbatar wa duniya da cewa dole aka yi yarjejeniya ne da manyan su saboda gwamnati ta nuna gazawa wajen damar da tsaro ga al’umma.

Faifan bidiyon ya nuna wani mutum cikin rawani da rufe ilahirin fuskar sa yana tambayar ɗaliban ko an taɓa lafiyar su ko an bar su da yunwa ko faɗa musu wata magana maras daɗi? Su kuma ɗaliban suna amsawa da cewa a’a ba a taɓa ba.

Saboda gwamnati ta gaza yanzu bayan an yi sulhu za mu mayar da ku ga iyayen ku. “Kamar yadda bidiyon ke nunawa”

Yanzu haka dai mutane suna kallon wannan yanayi na sace mutane don karɓar kuɗin fansa da kashe-kashen mutane da ake yi tare da kona gidaje da dukiyoyin su babu dalili ana ganin manyan jami’an gwamnati su ke da alhaki saboda waɗansu dalilai da suka bayyana kamar bayan janye jami’an tsaro bayan wani ɗan ƙaramin lokaci sai a kai hari da kuma idan aka kai hari ko an kira jami’an tsaro ba sa zuwa har sai an maharan sun gama cin karen su ba babbaka sannan sai ka ga jami’an tsaro sun zo suna harbin iska.

Musamman a irin abinda ya faru a makarantar ‘yan mata ta garin Maga da ke jihar Kebbi wanda a ke gani kamar wani wasan kwaikwayo ne aka shirya.

Gwamnatin Kebbi a ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Idris ta soma muna yatsa tsakanin ta da Sanata Garba Maidoki bayan ya fito ƙarara yana bai wa sojojin da aka girke domin bayar da tsaro ga ɗaliban lokacin da aka samu bayanan sirri dangane da kai hari a makarantar inda ya ke cewa ai doka ta bai wa jami’an tsaro ficewa idan suka fahimci an rinjaye su, saboda haka shi bai ga laifin jami’an tsaron ba.

Wannan maganar ba ta yi wa gwamnan jihar Kebbi daɗi ba saboda ba tana ganin ba zai yiwu ba a ce sun kasa neman wata mafita ga ɗaliban ba, saboda haka gwamnan ya ƙeƙasa kafa a ƙasa kan sai an binciko wane ne ya ba jami’an tsaron odar janyewa.

Yanzu haka dai al’ummar ƙasar nan sun gano cewa akwai yiwuwar gazawar gwamnati wajen samar da tsaro ga al’umma.

By ukarofi