Sai da ni za a iya magance matsalar tsaro a Zamfara – Matawalle

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Taƙaddama tsakanin Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Zamfara kan dabarun tsaro ta sake sabon salo, yayin da ƙaramin Ministan Tsaro, Muhammad Bello Matawalle, ya zargi gwamnan jihar, Dauda Lawal, da ƙoƙarin jingine shi a gefe duk da matsayinsa a Ma’aikatar Tsaro ta ƙasa. Don haka ya yi gargaɗin cewa, duk wani yunƙurin tsaro da ba a saka shi a ciki ba “ba zai haifar da ɗa mai ido ba.”

Matawalle, wanda ya yi wa’adin shekaru huɗu a matsayin gwamnan Zamfara kafin a naɗa shi minista, ya yi waɗannan zarge-zargen ne a wata hira da kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa, inda ya ce, Gwamna Lawal da gangan ya ƙi neman sa a lokacin da ya ziyarci Babban Ministan Tsaro a ofishinsu da ke Abuja duk da cewa shi ma yana ofis a lokacin.

“Ina wakilin Zamfara a Gwamnatin Tarayya,” inji shi, “ya kauce min, ya je wurin Badaru. Zan iya faɗa muku hakan ba zai haifar da komai ba.”

Idan za a iya tunawa, Gwamna Lawal ya sha bayyana yadda halin tsaro ya taɓarɓare a Zamfara, yana mai cewa, ya san mafakar ƙungiyoyin ’yan bindiga, kuma zai iya kawo ƙarshen matsalar cikin wata biyu — muddin jihar na da ikon umartar jami’an tsaro.

Gwamnan ya zargi jami’an tsaro da ke aiki a jihar da cewa, sau da yawa ba su ɗaukar mataki sai da umarni daga Abuja — lamarin da ya ce yana kawo cikas wajen kare rayukan jama’a.

Gwamna Dauda Lawal yana ƙoƙarin ganin an samar da ingantaccen tsaro a jihar, wanda hakan ya sa ya sama da Rundunar Kare Al’umma, wanda ake yi wa laƙabi da ‘Askarawan Zamfara’.

Zargin da Bello Matawalle ya yi na ɗauke da nauyin siyasa sosai, inda ya zargi wasu ’yan Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara da haɗa kai da ɓangaren Gwamna Dauda Lawal domin haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar. Matawalle ya yi gargaɗin cewa, mutanen da ke ɗaukar nauyin tayar da tarzoma a cikin APC ba za su daɗe cikin inuwa ba, domin a cewarsa, ba da jimawa ba za a fallasa su.

“A mazaunin gaskiya, APC haɗaɗɗiyar jam’iyya ce. Duk wanda ke haddasa rikici ana ɗaukar nauyinsa ne daga ɓangaren gwamnatin Dauda. Mun san su, muna da hujjoji a kan su, kuma za mu ɗauki mataki a lokacin da ya dace,” inji Matawalle.

Ya kuma ƙara da cewa, Gwamna Lawal na jin tsoronsa. “Duk abin da Dauda ya yi, sai ya ambaci sunana. Ko tuntuɓe ya ji, sai ya ce ni ne na jawo masa,” inji shi cikin barkwanci.

Masu lura da al’amura na ganin wannan musayar kalamai na nuna irin zurfin rikicin da ke tsakanin manyan jiga-jigan siyasa a Zamfara, rikici da ke ƙara dagula tsarin tsaro, musamman ganin yadda siyasa, muradun ɓangarori da rashin amincewa da juna tsakanin hukumomi ke haɗuwa waje guda. A cewarsu, irin wannan yanayi na iya gurgunta haɗin kan da ake buƙata wajen yaƙar matsalolin tsaro da ke addabar jihar.

By ukarofi