Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
A jiya Alhamis ne Kotun Ƙolin Nijeriya ta tsayar da ranar 15 ga watan Disamba domin yanke hukunci kan ƙarar da Gwamnatin Tarayya ta shigar a kan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta soke tuhumar da ake wa shugaban ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, tare da bayar da umarnin a sake shi.
A zaman sauraron ƙarar na jiya Alhamis, wasu mutane biyar na Kotun Ƙoli ƙarƙashin jagorancin Kudirat Kekere-Ekun sun dage sauraron ƙarar don yanke hukunci bayan ta ɗauki taƙaitaccen bayani daga lauyoyi daga ɓangarorin.
A yayin da take ci gaba da sauraron ƙarar, Ms Kekere-Ekun ta ce matakin da za a cimma a cikin ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar za ta magance batutuwan da ƙarar Mista Kanu ya gabatar na ƙalubalantar ci gaba da tsare shi.
Tun da farko, lauyan gwamnatin tarayya, Tijjani Gazali, Babban Lauyan Nijeriya (SAN), ya buqaci Kotun Ƙoli ta “ba da damar ɗaukaka ƙara” tare da yin watsi da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke na sakin Mista Kanu.
Mista Gazali wanda shi ne muƙaddashin daraktan faukaka ƙara a ma’aikatar shari’a ta tarayya da ke Abuja, ya roki kotun da ta tabbatar da hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke na ci gaba da tuhumar shugaban ‘yan awaren na Biafra.
Sai dai, lauyan Mista Kanu, Mike Ozekhome, farfesa a fannin shari’a kuma SAN, ya roqi kotun ƙolin “ta yi watsi da ƙarar da hukuncin tare da mutunta ƙarar da aka shigar domin yin adalci kan wannan lamari.”
Mista Ozekhome ya shaida wa kotun cewa wanda yake karewa yana tsare tun ranar 29 ga watan Yunin 2021, lokacin da aka dawo da shi Nijeriya.
“Muna cikin tawali’u muna kira ga Mai Shari’a da su yi watsi da ƙarar tare da yin ɗa’a da mutunta ƙarar da aka shigar domin yin adalci a kan wannan lamarin domin a saki Nnamdi Kanu wanda ke tsare tun ranar 29 ga watan Yuni, 2021. Ana tsare da shi ba bisa ƙa’ida ba a kan dokokin gida da na ƙasa da ƙasa,” in ji Mista Ozekhome.
Ya kuma shaida wa kotun cewa “babu wata gwamnati da za ta taka haƙƙin ‘yan ƙasarta.”
Tare da Ms Kudirat Kekere-Ekun, wacce ke jagorantar shari’ar, sauran mambobin kwamitin mai mutum biyar sun haɗa da Ibrahim Saulawa, Garba Mohammed, Tijjani Abubakar da Emmanuel Agim.
