
Kotun Ƙoli ta rusa afuwar da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, da aka samu da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello a shekarun baya.
A shekarar 2020, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya, hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar daga baya. Bisa dalilan jinƙai, Shugaba Tinubu ya rage mata hukuncin zuwa shekaru 12 kacal a gidan yari makonni kaɗan da suka gabata.
Saidai a yau, 12 ga Disamba, 2025, Kotun Ƙolin ta yi hukunci da rinjayen alƙalai huɗu, inda ta dawo da hukuncin kisa na farko da aka yanke mata tare ta tabbatar da shi.
Alkalai sun yi watsi da ɗaukaka ƙarar Sanda, suna masu cewa ba ta da wata hujja mai ƙarfi, tare da warware dukkan batutuwan da ta gabatar.
Yayin karanta hukuncin alƙalan, Mai Shari’a Moore Adumein ya jaddada cewa shaidu sun tabbatar da laifinta na kashe mijinta ba bisa ƙa’ida ba, kuma babu wata shakka a binciken.
Ya ƙara da cewa afuwar da aka yi mata ba ta dace ba, musamman kasancewar har yanzu ƙarar tana gaban kotu a wani lamari mai nasaba da kashe-kashe.
