
A ranar Alhamis Kotun Ƙoli ta yi watsi da ƙarar da gwamnatin Jihar Legas ta shigar game da shari’ar kisan gillar da aka yi wa Alhaja Kudirat Abiola, tare da tabbatar da sallamar tsohon Dogari Kuma Babban Jami’in Tsaron fadar shugaban ƙasa ma mulkin soji na Marigayin Janar Sani Abacha, wato Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya).
Alhaja Kudirat Abiola, matar Marigayi Cif M.K.O. Abiola da ake ganin shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 1993, ta rasa ranta ne a Legas a lokacin zanga-zangar da ta biyo bayan soke sakamakon zaɓen “June 12” wato 12 ga watan Yunin 1993 da aka gudanar a jihar Legas.
An zargi Al-Mustapha ne tare da ɗan Janar Sani Abacha, Mohammed Abacha da Lateef Shofolahan da laifin kashe Alhaja Kudirat Abiola.
Sannan, gurfanar da su a gaban Babbar Kotun Jihar Legas bisa tuhume-tuhume biyu da suka shafi haɗin kai wajen aikata kisa da kuma kisan Kudirat Abiola a ranar 4 ga Yuni, 1996.
A ranar 30 ga Janairun 2012, Babbar Kotun Jihar Legas ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Moji Dada ta same su da laifin kisan Kudirat Abiola, inda ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Saidai, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin a ranar 12 ga watan Yuli, 2013, tana mai cewa ɓangaren masu gabatar da ƙara bai gabatar da hujjojin da suka isa tabbatar da laifin akansu ba.
Daga bisani, gwamnatin Legas ta ɗaukaka ƙarar zuwa Kotun Koli, tana neman a dawo da hukuncin kotun farko, wato hukuncin kisa ga waɗanda aka ce an samu da laifin kashe Kudirat Abiola.
A shekarar 2014, Kotun Koli ta bai wa jihar legas izinin sake buɗe ƙarar duk da wa’adin shigar da ƙarar ya wuce.
Amma, a zamanta na wannan makon, Kotun Koli ta bayyana cewa gwamnatin Jihar Legas ba ta gabatar mata da wata takarda ko kuma ta wakilta lauya ba tun bayan samun izinin sake buɗe shari’ar.
