Tallafin Amurka ga Nijeriya: Yaƙi da ta’addanci ya wuce amfani da makamai

Spread the love

Daga ƙarshen watan Disamba na shekarar 2025 zuwa makonnin farko na Janairu 2026, alamu sun fara bayyana na yiwuwar samun sauƙi a matsalar tsaro da ta addabi Nijeriya tsawon lokaci. Tsawon kusan shekaru biyu, ƙasar ta rayu cikin yanayi mai cike da fargaba da rashin tabbas, tamkar yadda masanin falsafa Thomas Hobbes ya siffanta rayuwar da ba ta da tsari da kariya. Yau dai, ana iya cewa haske ya fara bayyana, ko da yake har yanzu akwai sauran rina a kaba.

Bayan harin sama da sojojin Amurka suka kai a daren Kirsimeti, wanda ya lalata wasu sansanonin ’yan ta’adda a sassan jihar Sakkwato, gwamnatin Donald Trump ta ƙara nuna goyon bayanta ga Nijeriya. Wannan ya zo ne ta hanyar tura muhimman kayan aikin soja domin ƙarfin gwiwar yaƙi da ta’addanci. 

Rundunar AFRICOM ta Amurka ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na ɗ, inda ta bayyana cewa an miƙa waɗannan kayayyaki ga hukumomin Nijeriya a Abuja. Wannan mataki ya nuna ƙarfin haɗin gwiwa a ɓangaren tsaro tsakanin ƙasashen biyu.

Tallafin ya zo ne a wani lokaci da Nijeriya ke ƙara zafafa yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci da masu garkuwa da mutane, musamman a Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da wasu sassan Tsakiyar ƙasar. Wannan ci gaba ya biyo bayan tattaunawar diflomasiyya da aka yi tsakanin Abuja da Washington a ƙarshen shekarar 2025. 

A watan Nuwamba na waccan shekarar, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta nemi taimakon Amurka a hukumance, biyo bayan matakin da Amurka ta ɗauka na sanya Nijeriya cikin jerin ƙasashen da ke da matsala ta musamman kan batun ’yancin addini.

Kwana kaɗan bayan wannan roƙo, aka gudanar da aikin haɗin gwiwa a ranar 24 ga Disamba, inda aka kai hare-haren sama kan sansanonin ’yan ta’adda a Arewa maso Yamma tare da goyon bayan hukumomin tsaron Nijeriya. 

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa wannan aiki ya samo asali ne daga haɗin kai a ɓangaren tsaro da musayar bayanan sirri tsakanin ƙasashen biyu. Ma’aikatar Harkokin Waje ta ƙara jaddada aniyar Nijeriya ta ci gaba da yin aiki tare da ƙasashen duniya wajen fuskantar ƙalubalen tsaro, tana mai cewa duk wani haɗin gwiwa yana gudana ne bisa ƙa’idar mutunta ikon ƙasa da dokokin ƙasa da ƙasa.

Bayan isar da kayan aikin soji, gwamnatin Amurka ta sake tabbatar da ƙudirinta na ƙarfin dangantaka da Nijeriya wajen yaƙi da ta’addanci da ‘yan bindiga. Wannan tabbaci ya fito ne daga jami’ar tsaro ta Amurka a Nijeriya, Laftanar Kanal Semira Moore, yayin ziyararta ga hedikwatar rundunar sojin ƙasa a Abuja. Ta bayyana cewa Amurka na da niyyar tallafa wa sojojin Nijeriya ba kawai ta fuskar yaƙi ba, har ma a ɓangaren jin ƙai da kula da walwalar jami’an tsaro, domin ƙara musu kwarin gwiwa da inganta aikinsu.

Sai dai duk da muhimmancin wannan tallafi na soja, wannan jarida na ganin ya dace a jawo hankalin gwamnatin Amurka kan buƙatar mayar da hankali ga ɓangaren da ba na soja ba. An sha bayyana cewa talauci, rashin aikin yi, ƙarancin ilimi, matsalolin kiwon lafiya da sauran ƙalubalen zamantakewa su ne manyan tushen da ke haddasa ta’addanci da rashin tsaro a Nijeriya. Idan ba a magance waɗannan matsaloli ba, to yaƙi da makamai kaɗai ba zai wadatar ba.

Ko da yake gwamnatin Tinubu na ƙoƙarin ɗaukar matakai wajen magance waɗannan ƙalubale, manufofin “America First” na gwamnatin Trump, wanda ya haifar da rage ko dakatar da tallafin ƙasashen waje, ya raunana ƙarfin Nijeriya wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaban zamantakewa da tattalin arziki. Wannan na iya janyo tsaiko ga ƙoƙarin da ake yi na shawo kan tushen matsalar tsaro.

Saboda haka, wannan jarida na kira ga gwamnatin Amurka da ta sake duba matakin rage tallafin ƙasashen waje gaba ɗaya, tare da la’akari da bai wa Nijeriya sassauci bisa halin da take ciki. Nujeriya na fama da ta’addanci da rashin tsaro da ke hallaka marasa galihu, ciki har da mata da yara. Magance wannan matsala ba zai yiwu ta hanyar makamai kaɗai ba, sai an haɗa da tallafin raya al’umma da inganta tattalin arziki.

A ƙarshen magana, yaƙi da ta’addanci zai samu nasara ne idan aka haɗa ƙarfi da ƙarfe, tare da magance tushen matsalolin da ke haifar da rikici a cikin al’umma. Wannan shi ne hanyar dawo da amincewa, zaman lafiya da walwala ga ’yan Nijeriya baki ɗaya.

By ukarofi