Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta umarci Yahya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi da ya gabatar da kansa gaban hukumar EFCC domin gurfanar da shi gaban kotu.
Kotun ta warware hukuncin babbar kotun jiha dake Kogi ta yi na hana EFCC kama Yahya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi ta Naira biliyan 80.
A wani hukunci na bai ɗaya da kotun ta yanke a ranar Talata, alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Ken Amadi ta dakatar da Yahya Bello daga ɗaukar wani mataki game da tuhumar da ake masa har sai an gurfanar da shi gaban kotu.
Hukumar EFCC ce dai ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da kotun jihar Kogi ta yi na hana kama Yahya Bello a watan Fabarairu.
A ranar 9 ga watan Fabarairu ne, kotun jihar Kogi ta dakatar da EFCC daga kamawa ko cin zarafin Yahaya Bello.
Tun wannan lokacin dai ake wasan ɓuya tsakanin Yahaya Bello da hukumar ta EFCC.
Kotun ɗaukaka ƙara ta bayyana hukuncin na kotun jihar Kogi a matsayin “Na Badaƙala”.
