Kowanne rubutu na da ikon canza tunanin mutum – Ɗanladi Z. Haruna 

Spread the love

(ƙarshen tattaunawar)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

MANHAJA: Ta yaya za a inganta kasuwancin littattafan Hausa ta hanyar zamani?

ƊANLADI: Don inganta kasuwancin littattafan Hausa ta hanyar zamani, ana iya amfani da fasahar intanet da sadarwa, kamar ƙirƙirar shafukan yanar gizo na musamman domin sayar da littattafai, da amfani da shafukan sada zumunta don tallata su, da kuma fitar da su a sigar e-books da audiobooks don sauƙaƙa isarsu ga masu karatu a duniya. Haka kuma, ana iya fassara littattafan Hausa zuwa wasu harsuna domin haɓaka masu karatu daga sassa daban-daban na duniya. 

Haɗin gwiwa tsakanin marubuta na gida da na duniya na iya ƙara jawo hankalin masu karatu tare da cusa al’adun Hausa cikin littattafan duniya. Bugu da ƙari, shirya tarurruka, bita, da gasar rubutu zai taimaka wajen ƙarfafa marubuta da masu karatu, yayin da tallafi ga marubuta zai ba su damar ci gaba da samar da sabbin littattafai masu inganci.

Akwai kuma buƙatar haɗin gwiwa da cibiyoyin ilimi domin shigar da littattafan Hausa cikin manhajojin makarantu da jami’o’i, tare da gudanar da tarurrukan karatu da nazari domin ƙarfafa al’adar karatu. Za a iya ba wa kamfanonin buga littattafai da masu siyarwa tallafi domin haɓaka hanyoyin rarrabawa da rage tsadar littattafai. Haka kuma, ƙirƙirar cibiyoyin karatu na musamman da shirya tarurrukan karatu zai taimaka wajen bunƙasa sha’awar karatu a cikin al’umma. A gefe guda, ana iya amfani da sabbin fasahohi kamar Artificial Intelligence (AI) da ɓirtual Reality (ɓR) don ƙirƙirar littattafai masu jan hankali a zamanance, wanda zai sa karatu ya zama mai daɗi da ban sha’awa.

Ta hanyar amfani da waɗannan dabaru, za a iya ƙara inganta kasuwancin littattafan Hausa da kuma haɓaka al’adar karatu da rubutu a cikin al’umma.

Kana ganin gasannin Gajerun Labarai da ýan siyasa ko ƙungiyoyi ke shiryawa suna da tasiri ga cigaban adabi?

Sosai ma kuwa, domin kuwa gasannin gajerun labarai da ‘yan siyasa ko ƙungiyoyi ke shiryawa suna taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa adabi da ƙarfafa marubuta. Irin waɗannan gasanni suna zaburar da marubuta su yi rubutu mai tsabta, mai ƙayatarwa, da kuma cike da ma’ana. Ta haka, marubuta suna ƙoƙarin ƙara inganta fasaharsu domin samun nasara, wanda hakan ke haɓaka ƙwarewarsu da kuma haɓaka adabin Hausa gaba ɗaya.

Baya ga hakan, gasannin na taimakawa wajen fito da sababbin marubuta waɗanda da ba a san su ba, tare da ba su damar samun shahara da kuma tallafi daga masu sha’awar rubuce-rubuce. Haka kuma, suna ƙarfafa tattaunawa kan al’amuran yau da kullum, musamman idan batun gasar yana da alaƙa da zamantakewa, al’adu, ko siyasa. Sakamakon haka, irin waɗannan gasanni na taimakawa wajen raya al’adar karatu da rubutu, da kuma wanzar da hikima a cikin al’umma.

Wanne saƙo ka ke da shi ga marubuta?

Saƙo na ga marubuta shi ne, ku ci gaba da rubutu, ku kuma ku amfani da basirar ku domin ba da labari, ilmantarwa, da kuma ƙarfafa al’umma. Rubutu wata hanya ce ta ƙarfafawa, wayar da kan jama’a, da kuma bayar da labari. Kowanne rubutu na da ikon canza tunanin mutum, ko kuma ya sa shi yin tunani mai zurfi. Don haka, ku riƙa amfani da kalmomi da basirarku don inganta rayuwar mutane da al’umma. Ku kuma ku ƙara ƙoƙari wajen inganta ƙwarewar ku, saboda rubutu ba shi da iyaka. Kowanne labari ko waƙa da kuka rubuta na iya zama hasken da zai haskaka hanyar wani.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka?

Zomo ba ya kamuwa daga zaune. Wannan karin magana na yi min daɗi ƙwarai domin kuwa tana nufin cewa idan mutum yana son samun nasara, dole ne ya yi aiki tuƙuru da ƙoƙari, ba zai yiwu kana zaune ka naɗe hannu ka samu abin da kake so ba tare da yin wani abu ba. Wannan magana tana ƙarfafa wa mutane cewar su yi amfani da ƙoƙarinsu da himma don cimma burinsu, maimakon su yi fatan abu ya zo musu ba tare da wani aiki ba.

By ukarofi