‘Yan Nijeriya miliyan 15 na fuskantar barazanar ambaliya, inji Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce aƙalla ƴan Nijeriya miliyan 15 ne suke fuskantar barazanar ambaliyar ruwan sama a yayin da daminar bana ke cigaba da ƙaratowa.

Shettima ya bayyana hakan ne a yayin taron Ɗaukar Matakan Kariya ga Annoba a Ƙasa a Cibiyar Aikin Daƙile Ta’addanci dake Ofishin Mai baiwa wa Shugaban ƙasa Shawara kan harkar Tsaro a Abuja, ranar Laraba.

Ya ce, suna ƙoƙarin bin hanyoyin da suka dace wajen ɗaukar matakan kariya don ganin an kauce wa faɗawa cikin iftila’in.

Shettima ya bayyana cewa, akwai buƙatar aiki kafaɗa-da-kafaɗa tsakanin hukumomin Gwamnatin Tarayya da na jihohi don magance matsalolin ambaliya a Nijeriya.

A shekarar 2024 ne madatsar ruwa ta Alau dake Maiduguri ta ɓalle, lamarin da ya haddasa asarar dukiyoyi da dama, inda ya ce a sanadin ambaliya an rasa kaso 5 na albarkatun kayayyakin gida na GDP.

Ya kuma ce, Shugaba Bola Tinubu ya amince da ware Naira biliyan 15 don bada agajin gaggawa ga iftila’in da ka iya aukuwa a wasu yankunan ƙasar.

Jihohin da ka iya fuskantar ambaliya sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-River, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Ribas, Sakkwato, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma Abuja.

Mataimakin Shugaban ƙasar a wani ɓangare, ya yi alla-wadai da munanan hare-haren da ƴan bindiga suka kai wa wasu yankunan Jihar Filato a ƴan kwanakin nan, ya na mai bayyana alhinin Shugaba Tinubu ga iyalan waɗanda lamarin ya shafa da daƙile ire-iren su a nan gaba.

By Babaji