Gwamnan Filato ya hana kiwon dare da taƙaita yawo da babur

Spread the love

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya sanar da haramta kiwo da dabbobi da dare da kuma taƙaita amfani da babura a faɗin jihar, sakamakon hare-haren da ake ta fama da su a yankuna daban-daban. A cikin wani jawabi da ya gabatar a ranar Laraba, gwamnan ya bayyana hare-haren da ake kaiwa a matsayin “tsare-tsaren ta’addanci” da nufin korar jama’a daga muhallansu na asali.

Mutfwang ya ce daga yanzu, ba a yarda a kwashe shanu da mota bayan ƙarfe 7 na dare ba, sannan kuma amfani da babura daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safe ya haramta har sai wani lokaci. Ya ce, “Jihar Filato ba za ta miƙa wuya ga tsoro ba, kuma ba za mu amince da wannan ɗabi’ar zubar da jini a matsayin sabon al’ada ba.”

Har ila yau, ya ce gwamnatinsa na ƙara azama wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma da tabbatar da doka a dukkan ƙananan hukumomin jihar. Ya kuma buƙaci al’umma da su bada haɗin kai wajen kare kansu cikin bin doka, yana mai cewa ba za a ci gaba da zubar da jini ba yayin da aka rasa aƙalla mutane 50 a harin baya-bayan nan da aka kai Kimakpa, ƙaramar hukumar Bassa .

By ukarofi