
Daga BELLO A. BABAJI
Biyo bayan ƙaddamar da ragin N15 ga kowacce litar man fetur a ƴan kwanakin nan, Matatar Ɗangote ta sake sanar da rage farashi, inda yanzu za a riƙa dakon kowacce lita akan N835 daga wajenta.
Hakan ya nuna an samu ragin N30 ga kowace lita daga N865 da ake sayar da ita a tsawon kwanaki shida da suka gabata.
Haka kuma ya nuna an samu jimillar ragin N45 daga yadda aka sayar da shi a ranar Laraba da ta gabata, wato ragin kaso 3.5.
Wannan shi ne karo na uku da Ɗangote ke rage farashi acikin makonni shida.
Hakan na ƙunshe ne a wata takarda da matatar ta fitar a ranar Laraba, inda ta ce matakin na daga cikin tsarin cajis da Hukumar Tace Ɗanyen Mai ta Ƙasa, NMDPRA ta ke yi a Nijeriya.
