Kuɗaɗen shiga na Katsina sun ƙaru daga Naira 400m zuwa Naira biliyan uku – Raɗɗa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Raɗɗa yace ci gaban ya samu ne sakamakon tace giɓin shiga da kuma amfani da tsarin TSA.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sanar da ƙaruwa a kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR) na jihar, wanda ya tashi daga kusan naira miliyan 400 zuwa naira biliyan 3 a kowane wata.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake karɓar tawagar kwamishinoni da ma’aikatan hukumar tattara kuɗaɗe, raba su da tsare-tsaren kuɗi ta ƙasa (Revenue Mobilization, Allocation and Fiscal Commission), ƙarƙashin jagorancin Sa’ad Ibrahim Bello, a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a fadar gwamnati da ke Katsina.

Gwamna Raɗɗa ya danganta wannan gagarumin ci gaba da gyare-gyaren tsarin kuɗi da gwamnatinsa ta aiwatar, musamman daƙile ɓarnar kuɗaɗen shiga (leakages) da kuma ƙaddamar da tsarin asusun baitulmali ɗaya (Treasury Single Account – TSA).

“Ta hanyar gyare-gyare na musamman, musamman daƙile ɓarnar kuɗaɗen shiga da kuma ƙaddamar da tsarin TSA, “mun samu ingantaccen ci gaba a harkar kuɗaɗen shiga,” in ji gwamnan.

Ya ƙara da cewa waɗannan gyare-gyare sun ƙarfafa gaskiya da rikon amana a dukkanin cibiyoyin gwamnati, tare da tabbatar da ingantaccen sarrafa dukiyar jama’a.

“Waɗannan matakai sun ƙara tabbatar da gaskiya da rikon amana a dukkanin hukumomin gwamnati,” ya ƙara.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta cika kusan kashi 90 cikin 100 na alƙawurran da ta ɗauka wa al’ummar jihar a lokacin yaƙin neman zaɓe.

“Mun cika kusan kashi 90 cikin 100 na alƙawurran da muka ɗauka wa al’ummar Jihar Katsina,” in ji shi.

Ya bayyana cewa nasarorin sun shafi fannoni daban-daban da suka haɗa da noma, ilimi, ƙanana da matsakaitan sana’o’i (MSMEs), gyaran aikin gwamnati, da kuma tsaro.

Dangane da tsaro, ya ce zuba jarin da gwamnati ke yi ya haifar da sakamako mai kyau, inda aka samu raguwar matsalolin tsaro a faɗin jihar.

“Zuba jarin da muka yi a fannin tsaro ya haifar da sakamako mai ma’ana, inda aka samu raguwa sosai a matsalolin tsaro,” in ji shi.

By ukarofi