Daga USMAN KAROFI
Babbar Alƙalin Alƙalai ta Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bayyana cewa wasu alƙalai na ɓata sunan ma’aikatar shari’a a ƙasar.
Yanke hukunce- hukunce masu jawo cece-kuce daga kotuna masu matsayi ɗaya ya tayar da ƙura a lokuta daban-daban, musamman a Kano da Ribas, inda ake fama da rikici tsakanin manyan ‘yan siyasa.
Da take jawabi a wajen wani taron tattaunawa ,Kekere-Ekun ta ce duk da wannan ƙalubale, ma’aikatar shari’a a Nijeriya na da alƙalan da ke da ƙwazo da gaskiya.
Ta jaddada cewa Nijeriya na da alƙalai ƙwararru kuma masu aiki tuƙuru, tana jan hankalin alkalai cewa su tuna cewa suna da alhakin kansu da Allah a matsayinsu na mutane.
Kekere-Ekun ta bayyana cewa tushen adalci na samun tasiri daga addinai da ake bi a ƙasar, inda ta ce duka addinin Musulunci da Kiristanci na koyar da halaye nagari da gaskiya.
