Ku kare martabar dimokraɗiyya – Janar Musa ga takwarorinsa na ECOWAS

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugaban Ma’aikatan Tsaro na Nijeriya, Janar Christopher Musa ya yi kira ga takwarorinsa na ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS da su kare martabar dimokraɗiyya gwargwadon yadda dokokin ƙasashensu su ka shar’anta.

Ya ce, faruwar juyin mulkin soji a ƙasashen yammacin Afirka sun haifar da barazana ga martabobi da darajojin demokraɗiyya.

Blueprint ta ruwaito cewa, sojoji sun yi wa farin hula juyin mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar cikin shekaru uku da su ka gabata.

Janar Musa ya faɗi hakan ne a yayin ganawa da shugabannin tsaro na ƙasashen ECOWAS a Abuja a ranar Laraba, ya na mai cewa juyin mulki abu ne mai nuna gazawa ga sauke nauyinsu na ƙwararrun sojoji, don haka ya ce dole su ƙaurace masa.

Ya ƙara da cewa, zaman nasu zai taimaka wajen dakatar da aukuwar juyin mulki tare da samun wanzuwar zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa ga ƴan ƙasashen yammacin Afirka.

By Babaji