Aƙalla mutane ashirin ne suka rasa rayukansu yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga harin ‘yan bindiga a ƙauyen Kali da ke ƙaramar hukumar Gummi a jihar Zamfara bayan kwale-kwalen su ya nutse.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun kewaye ƙauyen da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Lahadi da ta gabata.
“‘Yan bindigar a ranar Lahadi da ta gabata an ga sun nufi ƙauyen Kalli da babura ɗauke da manyan makamai domin kaiwa yankin hari, wanda hakan ya sa mutanen ƙauyen su ka tsere,” inji shi.
Ya ce kwale-kwalen ya cika da mutane sannan ya nutse a cikin Kogin Birnin Magaji wanda hakan ya kai ga mutuwar mutane 20. Ya ƙara da cewa an gano gawarwakai biyar a Kogin Falale, huɗu a Kogin Birnin Magaji, yayin da aka kuma gano gawa uku a Kogin Gadar Gummi yayin da suke ƙoƙarin tserewa zuwa ƙauyen Iyaka.
“Kamar yadda nake magana da kai yanzu, an gano gawarwakai 12 kuma an sake gano wasu shida a ranar Laraba waɗanda suka rasa rayukukansu sakamakon nutsewar kwalekwalen nasu yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga harin ‘yan bindiga a ƙauyen Kali da ke ƙaramar hukumar Gummi.”
