Kungiyar ƙananan ƙabilun Arewa sun gargaɗi El-Rufai ya shiga taitayinsa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kungiyar ƙananan ƙabilu na Arewacin Nijeriya (NNMG) ta yi Allah-wadai da kakkausar murya da zargin da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu na da niyyar tsawaita wa’adin mulkinsa fiye da shekarun da kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

A fahimtarmu tsohon gwamnan, wanda yanzu ya koma ɗaya daga cikin masu kokarin kawo ruɗani da hayaniyar siyasa a ƙasar, kawai yana magana ne saboda ƙiyayya, bakin ciki da kuma rashin mutunta dimokuraɗiyya.

Idan ba a manta ba, Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya kai wa El-Rufai ziyarar jimamamin hari da aka kai wa ‘yan jam’iyyar ADC a Kaduna yayin wani taro da jam’iyyar ta yi.

A lokacin ziyarar ne El-Rufai ya gargaɗi ‘yan Nijeriya da ‘yan siyasar Nijeriya cewa idan ba a fa ankare ba Tinubu zai iya kin ba da mulki bayan wa’adinsa ya cika.

Waɗannan kalamai ne ya sa wannan kungiya ta maida wa El-Rufai martanin cewa ya shiga taitayinsa tun da wuri.

A cewar ƙungiya, tun bayan rasa samun muƙami a gwamnatin Tinubu El-Rufai ya zama karen farautar jam’iyyun adawa inda ya shiga gaba wajen caccakar gwamnatin Tinubu da duk wani abu da ya sa a gaba.

”A iya sanin mu, El-Rufai ya ƙware wajen cin amana da yaudara ba tun yanzu ba, tun a tsawon mulkinsa na gwamnan Kaduna

ƙungiyar ta ce kundin tsarin kasa ya ƙayyade tsawon wa’adin mulkin shugaban ƙasa a Nijeriya, saboda haka ƙoƙarin kawo ruɗani da tada hankali jama’a da zargin cewa wai Tinubu na so ya zarce fiye da wa’adinsa da doka ta gindaya masa ba za ta saɓu ba.

Don haka ƙungiyar ta gargaɗe shi da ya iya wa bakinsa tun da wuri, ya shiga taitayinsa.

A ƙarshe sun umarce shi da ya baiwa ‘yan Nijeriya haƙuri sannan kuma sun yi kira ga jami’an tsaro su dallarawa tsohon gwamnan tocila, su rika bin sahun sa duk inda ya bi.

By ukarofi