Kwanan Bello Turji ya kusa ƙarewa – Janar Musa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya tabbatar da cewa kwanan nan za su kama shahararre kuma jagoran ƴan bindiga, Bello Turji yayin da jami’ai ke ƙara kusantarsa inda ya ke ɓuya a dazukan Jihohin Sakkwato da Zamfara.

A lokacin da ya ke magana a taron bikin cikar shekara 38 na makarantar Kwalejin horo ta sojoji a Kaduna, Janar Musa ya ce maganar kama Turji abu na wani lokaci wanda a halin yanzu hukumomin tsaro na aiki tare wajen ganin ɗan ta’addan ya shiga hannun doka.

Ya ce, “Mu na bibiyar Bello Turji. Abu ne na wani lokaci kafin mu kai gare shi. Ba shi da wani wajen da zai ɓuya.”

Janar Musa ya ce, ƙoƙari da sojoji da sauran hukumomin tsaro ke yi, hakan na faruwa ne don kawo ƙarshen ƙalubalen tsaro musamman a yankin Arewa-maso-Yamma.

Ya kuma yi kira ga al’ummar Nijeriya su kasance masu zaman lafiya da bada haɗin-kai, ya na mai cewa matsalar rashin tsaro abu ne da ya zama ruwan dare duk da ci-gaba da aka samu ta fuskar fasahar zamani.

Ya ƙara da kira ga ƴan ƙasa da su aiko da saƙon duk wani abun zargi da suka gani ga jami’ai, ya na mai neman su da ƙaurace wa taimakawa ɓarayi a garuruwansu kasancewar sai da haɗin-kansu ne za a samu nasarar kawo ƙarshen rashin tsaro.

By Babaji