Kwara: An samu kuɗaɗen ƙasar waje da wuƙa a hannun mabarata yayin kame

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Kwara ta ƙaddamar da atisayen kamen masu bara a titunan manyan unguwannin babban birninta, wato Ilorin, inda aka kama kimanin mabarata 40 a tsakiyar mako.

A yayin haka ne aka ƙwato wasu ababen ban-mamaki da suka haɗa da tsabar kuɗaɗe ciki har da Dalar Amurka da nairorin Nijeriya da jimillar adadinsu ya kai kusan N100,000 da kuma wata wuƙa mai kaifi.

Ma’aikatar Walwalar Al’umma da Ci-gaba da haɗin-gwiwar jami’an Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS) reshen jihar suka ƙaddamar da aikin kamen a yankunan Tipper Garage, Tank, Offa Garage da Shataletalen Geri Alimi.

Jami’ai a yayin bincike sun kama wani mai suna Musa Mahmud daga Jihar Kano, inda aka same shi da tsabar kuɗi na Dalar Amurka da kuɗin Nijeriya sama da N18,000. Haka ma wani Malam Aliyu Buhari shi ma daga Kano, wanda aka same shi da sama da N17,000.

Ana haka ne kuma aka ga wani daga cikinsu ɗauke da wuƙa mai kaifin gaske, inda ya yi ikirarin cewa yana amfani da ita ne kaɗai wajen yanka albasa.

Daga cikin waɗanda aka kama, akwai guda bakwai da da an kama da irin laifin, huɗu mata da maza uku, waɗanda a karo na biyu kenan ake kama su a wajen da aka hana su yin bara.

By Babaji