Kwara: Za a rataye shi bayan samun sa da laifin kisan ƴar ajin ƙarshe a Kwalejin Ilimi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotu da ke zaune a Ilorin, babban birnin Jihar Kwara, ta yanke wa wani Abdulrahman Bello hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin halaka Hafsoh Lawal, wadda ƴar ajin ƙarshe ce a Kwalejin Ilimi da ke birnin.

Da ta ke gabatar da hukunci kan lamarin a ranar Alhamis, Mai Shari’a Hannah Ajayi ta kuma ta wanke wasu mutum huɗu da ake tuhumar su da hannu a aikata laifin.

Mutane huɗun sune: Ahmed Abdulwasiu, Jamiu Uthman, Suleiman Muyideen da Abdulrahman Jamiu waɗanda da fari aka alaƙanta su da kisan marigayar.

A yayin yi wa mai laifin hukunci wato Abdulrahman Bello, wanda malamin makarantar Islama ne, Alƙalin ta bayyana kisan a matsayin abinda aka yi bisa rashin tausayi da ya kai maƙura wajen mugunta.

Ta ce, hujjoji sun bayyana cewa an kashe Hafsoh ne domin yin asirin kuɗi da ita da sayer da sassan jikinta.

Alƙalin ta ƙara da cewa, malamin ya yaudare ta ne da nufin yana son ta da aure, inda ya gayyace ta gidansa da mummunar manufa domin samun damar halaka ta.

A ranar 10 ga watan Fabarairu, 2025 ne aka aiwatar da laifin bayan mai laifin ya gayyaci marigayar gidansa inda ya yi lalata da ita, sannan ya kashe ta kuma ya daddatsa gangar jikinta.

Yayin da aka kama shi kuma ake gudanar da bincike akansa, an gano wani kwalba da ke cike da jini da wasu ababen marigayiyar gami da addar da ya yi amfani da ita wajen sassara ta a ɗakinsa.

Kazalika, daga bisani an gano gawarta a wani wajen zubar da shara da ke kusa a garin na Ilorin.

By Babaji