
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar Ƙwallon ƙafa ta Galatasaray ta sanar da Victor Osimhen na Super Eagles a matsayin sabon ɗan wasanta, lamarin da ke nuna ta samu gagarumar nasara a shirinta na shiga sabuwar kakar wasa.
A yayin gabatar da ɗan wasan, Shugaban ƙungiyar, Dursun Aydin Özbek da mataimakinsa Abdullahi Kavukcu sun bayyana jin daɗinsu da ɗan wasan ya amince da koma wa ƙungiyar da taka leda bayan zaman ɗan wasan aro a ƙungiyar daga Napoli a kakar da ta gabata.
A nasa jawabin, Osimhen ya bayyana komawar tasa a matsayin dawo wa gida, inda ya ce zai yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen kai Galatasaray ga nasara.
Ana ganin ɗan wasan zai ƙara wa tawagar ƴan wasan gaba na ƙungiyar ƙarfi gami da ƙarfafa mata a yunƙurinta na lashe kofuna.
