Yobe: Sarkin Gudi, Alhaji Isah Bunuwo ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sarkin Gudi a Jihar Yobe, Alhaji Isah Bunuwo Madugu Ibn Khaji ya rasu bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.

Sakataren Masarautar Gudi a garin Gadaka da wasu iyalan marigayin suka tabbatar da rasuwarsa a ranar Alhamis a Asibitin Nizamiye da ke Abuja.

Za a yi jana’izar marigayin, wanda shi ne Sarkin Masarautar na 19 a yau Juma’a.

Kamar yadda masarautar ta sanar, za a yi janazar ne da misalin ƙarfe 2 na rana a garin Gadaka da ke Ƙaramar Hukumar Fika a jihar Yobe.

By Babaji