Ouattara Ya sake fitowa takara: ko tarihi zai maimaita kansa a Ivory Coast?

Spread the love

Shugaban ƙasar Ivory Coast, Alassane Ouattara, mai shekaru 83, ya sanar da cewa zai sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na watan Oktoba mai zuwa, lamarin da ya tayar da jijiyoyin wuya a ƙasar.

Ouattara wanda ke kan mulki tun 2011, ya ce: “Ina da cikakken lafiyar da zan ci gaba da shugabanci, kuma tsarin mulkinmu ya ba ni dama.” Ya ce ƙalubalen tattalin arziki da tsaro na buƙatar gogaggen jagora kamar sa.

Sai dai wannan matakin ya ƙara raba kan al’umma, duba da yadda shahararrun ‘yan adawa kamar Laurent Gbagbo, Guillaume Soro da Charles Blé Goudé ke haramta shiga takara, wasu saboda hukuncin da kotu ta yanke musu, wasu kuma saboda batun ƙasa.

Babban abin da ke jawo cece-kuce shi ne, ko Ouattara yana da hurumin sake tsayawa takara bayan wa’adin da ake ganin ya cika. ƙungiyoyin adawa irin su PPACI da PDCI na kira da a janye taƙaitaccen tsarin da ya ke hana wasu shiga.

Masu sharhi na ganin ana dab da sake komawa irin rikicin 2010–2011 da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 3,000. Tuni ake hasashen zaɓen na bana zai kasance mai cike da ruɗani da yuwuwar tarzoma.

By ukarofi