Ghana ta tura sojoji bayan harin da ya kashe ɗalibai a iyakar Burkina Faso

Spread the love

Gwamnatin Ghana ta ɗauki matakin gaggawa na tura sojoji zuwa garin Bawku da ke kan iyakar ƙasar da Burkina Faso, bayan harin da ya yi sanadin mutuwar dalibai uku.

Feliɗ Kwakye Ofosu, mai magana da yawun shugaban ƙasa, ya ce gwamnati ta canza matsayinta daga “tsare zaman lafiya” zuwa “tilasta zaman lafiya” saboda ƙara tsanantar rikicin.

Garin Bawku na fama da rikicin sarauta da ke tsakanin ƙabilun Mamprusi da Kusasi, kuma ana fargabar rikicin zai buɗe ƙofa ga ‘yan jihadi daga yankin Sahel. Ghana ta ce, ana ci gaba da sintiri a makarantun yankin tare da kakaɓa wa yankin dokar hana fita daga 2 na rana zuwa 6 na safe.

A shekarar 2023, an tura ƙarin sojoji dubu ɗaya a garin bayan kisan jami’in shige da fice. Ghana na ƙara tsaurara matakan tsaro domin hana shigowar matsalolin tsaro daga Burkina Faso.

By ukarofi